Sabanin ra'ayoyi kan aikin Majalisar Dinkin Duniya
October 24, 2016
Duk da cewa akwai da dama da suke yaba Majalisar Dinkin Duniya wajen gudanar da ayyukan agaji da jin kai da habaka ilimi da kiwon lafiya a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, amma yawanci al'ummar wannan shiyya basu bayyana gamsuwa da ayyukanta ba saboda a cewarsu tana fifita wasu kasashe a kan wasu.
A cewar kungiyoyin fararen hula da yawancinsu suke aiki da bangarorin Majalisar Dinkin Duniya ya zama dole a jinjina wa kokarinta a dukkanin ayyukanta na taimaka wa bani Adama. Ibrahim Yusuf da ke shugabantar gamayyar Kungiyoyin fararen hula naj ihar Gombe ya na daga cikin masu wannan ra'ayi. Sai dai akwai wadanda suke ganin a tsarin Majalisar Dinkin Dunyia, wasu kasashe na zama shafaffu da mai inda duk abin da suka yi sai a goyi bayansu. Ahmad Usman Gombe wani mai fashin baki kan harkokin yau da kullum na cikin masu irn wannan fahimta.
Shi ma Honorable Adamu Musa Dan Amar wanda ya yaba da ayyukan Majalisar Dinkin Duniyar ya kuma nuna cewa rashin daukar tsattsauran mataki da zai kai ga kawo karshne rikcin Gabas ta Tsakiya da kuma kin daukar matakin samar da kasar Falasdinawa na daga cikin wuraren da majalisar ta kasa.
Masana harkokin dipolomasiyya sun nuna cewa tafiyar majalisar na neman gyara da daidaito tsakanin kasashe musamman ganin yadda wasu kasashe suka fara dawowa daga rakiyarta inda wasu kasashen nahiyar Afirka suka fara neman fita daga yarjejeniyar da ta kafa kotun duniya saboda yadda ake zargin ta dauki bangare.