1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ostireliya ta gano magungunan fargaba

July 4, 2023

Ostireliya ta zama kasa ta farko a duniya da ta amince da amfani da irin magungunan da ke tasiri a kan hankalin dan adam wajen warkar da masu fama da damuwa.

MDMA Pillen
Magungunan MDMA Hoto: Jonas Roosens/Belga/dpa/picture alliance

Yayin da wasu likitoci ke ganin kamar an yi hanzarin daukar matakin tunda maganin na iya haddasa hauka, masana kimiya sun ce wannan babbar ci gaba ce a fannin kula da lafiyar kwakwalwa.

Wakilin hukumar kula da ingancin abinci da magungunan Ostireliya ke nan wanda sanar da cewa daga daya ga watan Yuli duk likitocin kwakwalwar dake da rajista za su iya amfani da magungunan da ke iya tasiri kan tunani da hankalin mutum wajen warkar da masu fama da matsalolin da ke da nasaba da kwawalwa.

Magunguna biyu ne aka amince da su. Sun hada da MDMA da Psylocybin wanda ake samu a mushrooms ko kuma naman gwari. Dr Brad McKay na daga cikin likitocin da suka yaba da wannan cigaban wanda y ace akwai babban bukatar magungunan.

kwayoyin maganin MDMA Hoto: Fernando Vergara/AP/picture alliance

Akwai mutane da yawa da ke fama da damuwa mai tsanani wadda ba ta jin magani, kuma in banda magungunan da aka saba bayarwa na hana damuwa, bamu da wani zabi mai nagarta sai yanzu shi ya sa hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta halata magungunan wadanda ta ce za'a bayar a wuraren da likitoci za su iya lura da duk abubuwan da ke faruwa dan wadanda suke cikin damuwar su sami wani zabin da zai taimaka musu.

Ba wannan ne karon farko da ake amfani da ire-iren magungunan ba. Shekaru 50 da suka gabata an yi amfani da da su wajen warkar da masu fama da tabin hankali domin ya kan bude hanyoyin kwakwalwar da sukan dushe ne, kafin gwamnatoci suka haramta bisa dalilai na siyasa, tare da zargin cewa miyagun kwayoyi ne saboda suna yawan wasa da hankalin mutun kuma sukan kawo sauyi a yanayin fahimtar abubuwa da yadda mutun zai rika ji a jikin shi da ma yadda zai iya koyon abubuwa sa'annan suna iya ruda mutum, su sa shi gani da sauraren abubuwan da ba su ne ba hatta lokaci ma wata sa'a sai ya birkice wa mutum.

Sai dai a cewar David Nutt likitan kwakwalwa ne wanda shi da kansa ya gwada magungunan ya ce bayan an bayar da maganin sukan duba kwakwalwa da nau'rar daukar hoto kuma yawanci sukan ga cewa kwakwalwar ta saki ba ta fama da matsin lambar da suka gani da farko.

Ba kamfanoni ke sayar mana da magungunan ba. Duk likitan da ya cancanta zai samu sai ya yi amfani da kwarewarsa ya bai wa wanda ya dace bisa sharuddan da aka gindaya kamar bai wa wadanda maganin da aka saba bayarwa bai yi musu aiki ba, kuma a gani na hadarin kalilan ne domin alfanun da za'a samu musamman a wadanda ke da damuwa har suke tunanin kashe kan su, na da yawa sosai.

Sadda aka yi amfani da shi a baya, masana kimiyya sun gwada maganin kan masu fama da lalurar wajen sama da dubu 40 kuma an wallafa kasidu da yawa wadanda duk suka bayyana sahihancin magungunan. Sakamakon ya nuna cewa a karon farko an sami maganin da ke iya tasiri a kan hankalin dana dam, bacin haka maganin na iya kawo sauyi a masu fama da damuwa, da yawan fargaba da masu shaye-shaye.

Leman kwado da ake magunguna da shiHoto: Arnaud Journois/dpa/MAXPPP/picture alliance

To yaya maganin ke aiki? David ya ce a kan bai wa mai fama da lalurar maganin ne dan kadan ya sha sai ya sa shi baci inda zai yi mafarki ko kuma dai ya fita hayyacinsa. A mafarkin ne zai tinkari ainihin abun da ke kawo mi shi damuwar kuma da zarar ya dawo cikin hayyacin shi sai a ga cewa komai ya gyaru.

Ba wanda ya taba dawowa hayyacinsa ya cigaba da damuwa, kusan kowa yak an sami sauki, sai dai idan damuwar ta dade a jikin mutun sai an dan dauki lokaci ana ba shi maganin amma duk da haka yawancin wadanda ke shiga yanayin mafarkin kan sami sauki sosai su ma dade su yi watanni ba tare da matsala ba.

Dole sai mutun ya shirya domin idan mutun ya yi amfani da magungunan da tsoro za'a iya samun akasi. Haka nan kuma wadanda suke da hauka a zuri'arsu bai kamata a ba su ba domin zai iya asasa haukar a maimakon kawo sauki. Shi ya sa aka ce dole sai likitocin da mahukunta suka amince da su za su iya bayar da magungunan.