1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Sabbin hare-haren Isra'ila sun sa 'yan Lebanon tserewa

Mouhamadou Awal Balarabe
September 25, 2024

Isra'ila ta yin ruwan bama-bamai a kasar Lebanon a rana ta uku a jere, lamarin da ya yi sanadin kaurace wa dubban mutane daga kudancin kasar, a daidai lokacin da kasashen duniya ke kokarin kauce wa barkewar sabon rikici.

Libanon Sidon | Flucht wegen israelischer Luftangriffe
Hoto: Mohammed Zaatari/AP Photo/picture alliance

Babu alkaluma kan yawan fararen hula da suka jikkata a Lebanan a sabbin hare-harten Isra'ila a rana ta uku a jera a kasar Lebanon, amma dai kungiyar Hezbollah ta tabbatar cewa kwamandanta daya Ibrahim Mohammed Kobeissi ya mutu, a wani harin bam da Isra'ila ta kai a yankin kudancin Beirut a ranar Talata. Sai dai a martanin da ta mayar, Hezbollah ta harba kusan rokoki 300 zuwa cikin kasar Isra'ila, wadanda suka raunata fararen hula da sojoji shida.

Karin bayani: Zaman tankiya kan iyakar Lebanon da Isra'ila

Jakadan Isra'ila a Majalisar Dinkin Duniya Danny Danon ya ce kasarsa ba ta da sha'awar mamaye kasar Lebanon, kuma tana fifita hanyar diflomasiyya wajen kawo karshen rikicinta da Hezbollah. Dama dai, damuwa kan ta'azzarar rikici tsakanin Isra'ila da Hezbollah ne ya mamaye bude taron Majalisar Dinkin Duniya a birnin New York.  A wannan Laraba ne, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yi taron gaggawa kan rikicin Isra'ila da kungiyar Hezbollah bisa bukatar Faransa, saboda ka da Lebanon ta zama fagen yaki kamar Zirin Gaza.