1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Sabbin manufofin ketare na taka rawa a zaben Jamus

Jens Thurau Zainab Mohammed/Mouhamadou Awal
February 21, 2025

Shugaban gwamnatin Jamus da za a samar a zaben tarayya na 2025 zai yi wani sabon tsari a kan manufofinsa na ketare, inda zai nisanta kansa daga Amurka tare da rungumar tsarin samar wa kasa tsaro.

Olaf Scholz na jam'iyyar SPD da Friedrich Merz na jam'iyyar CDU na daga cikin manyan 'yan takara a zaben Jamus na 2025
Olaf Scholz na jam'iyyar SPD da Friedrich Merz na jam'iyyar CDU na daga cikin manyan 'yan takara a zaben Jamus na 2025Hoto: Michael Kappeler/dpa-Pool/dpa/picture alliance

Sabuwar gwamnatin Jamus za ta fuskanci kalubale masu tarin yawa a kan manufofinta na ketare bayan sabon zaben 2025. Akwai batu na sauyin alkibla, wadanda akasarinsu za su kasance sabbi a fannoni daban-daban, inda Jamus za ta yi ban kwana da rawar da take takawa na matsayin kasa mai fada a ji kuma mafi karfin tattalin arziki a tnahiyar Turai.

Karin bayani:Muhawara mai zafi gabanin zaben Jamus

Shekaru da dama bayan yakin duniya na biyu, ministocin harkokin wajen Jamus sun yi tsammanin za su kasance a kan matsayinsu mai martaba, na jan akalar lamuran da suka danganci Turai. Duba da dangantakarta da kasashen yammacin duniya, Jamus ta ci gaba da zama mai ra'ayin bangarori daban-daban, kana mai fafutukar tabbatar da dimukuradiyya da bin doka da oda, inda ake zartar da shawarar manufofin harkokin waje tare da hadin gwiwar abokanta na Yamma, yayin da Amurka ke da alhakin tsaron kasar.

Amma ya ya labarin yake a yanzu?

A taro kan tsaro na birnin Munich, sabon mataimakin shugaban Amurka J.D. Vance ya sanar da cewa dole ne Turai ta dauki nauyin tsaron kanta.  Wannan magana ce da ta bata ran shugaban jam'iyyar CDU  kuma wanda ake ganin zai iya zama sabon shugaban gwamnati Friedrich Merz.

Friedrich Merz ya yi Allah wadarai da shisshigin Amurka a zaben JamusHoto: Kay Nietfeld/dpa/picture alliance

A wata hira da tashar DW, Merz ya ce: "Eh, lallai yau ranar tarihi ne a gare mu. Ana dasa ayar tambaya game da tsayawar Amurka kuma Amurkawa na saka shakku game da nuna dimukuradiyya. A bayyana yake, ana mana katsalandan a cikin zaben, ciki har da yadda ake tafiyar da jam'iyyun dimukuradiyya da sauran su. Kuma dole in ce, abun damuwa ne. Ban yi mamaki wannan sanarwar ba."

Karin bayani: Jamus: Farin jinin CDU da CSU ya ragu gabanin zabe

Duk wannan yana faruwa ne a cikin sauri. Roderich Kiesewetter da ke zama kwararre kan harkokin waje na kungiyar 'yan majalisu ta jam'iyyar CDU, na ganin cewar kasar Jamus hali na cikin tsaka mai wuya. Ya zama wajibi Jamus ta fahimci cewa tsarin mulkin dimukuradiyya da tsarin mulkin shi kansa na kara fuskantar barazana. Alal misali, a halin yanzu kasar Chaina tana yin duk abin da za ta iya don fadada tasirinta, da kuma kara dogaro da kasashen dimukuradiyya kamar Jamus ke yi da ita.

Ko da idan aka zo ga batun da ya ke daukar hankali a halin yanzu na manufofin Ukraine, babu abin da zai ci gaba da  kasancewa kamar a da. Bayan yakin Rasha da Ukraine tun daga bazarar  2022, Jamus ita ce babbar mai goyon bayan Ukraine bayan Amurka, ta hanyar soja da kuma ta fuskar daukar 'yan gudun hijira.

Sojojin zaman lafiya na Jamus a Ukraine?

Farin jinin shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ragi idan aka kwatanta da zaben da ya gabata.Hoto: Kay Nietfeld/dpa-Pool/picture alliance

Shugaban gwamnati na yanzu Olaf Scholz ya ce da kamar wuya a iya aiwatar da shi a zahiri, inda ya ce: "Dole ne mu ci gaba da tallafa wa Yukraine, dole ne kuma ta samu tabbacin dogaro da mu na cewa hakan zai kasance. Muna maraba da cewar, ana tattaunawa kan batun zaman lafiya. Amma dole ne mus an halin da ake ciki game da wannan yunkuri, kuma dole a yi la'akari da matayin Ukraine na yarda da abin da aka gabatar mata."

Karin bayani: Jamus ta soki Elon Musk yi mata katsalandan

Yanzu akwai barazanar yiwuwar cimma yarjejeniyar kawo karshen yakin Ukraine, wanda mai yiwuwa Amurka da Rasha ne kawai za su yi tattauna. Jamus da sauran kasashen Turai, su ne ke da alhakin tabbatar da aiwatar da yarjejeniyar da sojojinsu. Ko ta ya ya dai, shugaban Amurka Donald Trump ya riga ya bayyana cewa, wajibi ne a kawo karshen yakin.


 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani