1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Tattalin arziki

Jamus ta kaddamar da sabbin manufofi kan China

Suleiman Babayo MA
July 13, 2023

Gwamnatin kawance Jamus ta bayyana sabbin manufofiun cinikayya da China domin rage kasadar da kasar za ta fuskanta a bangaren kasuwanci na duniya.

Annalena Baerbock ministar harkokin wajen Jamus da Qin Gang takwaranta na China
Annalena Baerbock ministar harkokin wajen Jamus da Qin Gang takwaranta na ChinaHoto: Michael Kappeler/Pool via REUTERS

Gwamnatin Jamus ta bayyana sabbin manufofin cinikayya da kasar China, bayan tattaunawa tsakanin jam'iyyun da ke cikin gwamnatin kawancen ta Jamus, inda aka amince da rage kasadar da ke cikin cinikyayya da China, wadda take zama babbar abokiyar cinikayyan Jamus.

Annalena Baerbock ministare harkokin wajen kasar ta Jamus ta bayyana manufofin a cibiyar kula da harkokin China da ke birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus. Sannan Baerbock  ta kara da cewa Jamus tana bukatar aiki da China, amma China kuma tana bukatar kasashen Turai. Yanzu Jamus ta dauki matakin karfafa zuba jari a wasu kasashen duniya masu samun tagomashin tattalin arziki.

Sabbin maniufofin za su taimaka wa Jamus wajen rage dogaro da China, tare da samun kayayyakin masana'antu daga wasu bangarorin na duniya.