1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin matakan tsuke bakin aljihu a Spain

July 11, 2012

Spain ta sanya ƙarin haraji a matsayin wani ɓangare na matakan shawo kan matsalar koma bayan tattalin arziƙi.

Spain's Prime Minister Mariano Rajoy opens his briefcase at the start of a parliamentary session in Madrid, July 11, 2012. Rajoy said on Wednesday he would raise the value-added tax by 3 percentage points to 21 percent as part of a large package of tax hikes and spending cuts aimed at trimming the public budget by 65 billion euros over the next 2-1/2 years. With the economy in recession, unemployment high and tax income falling, Spain is struggling to meet tough deficit cutting targets that it has agreed on with the European Union. REUTERS/Andrea Comas (SPAIN - Tags: BUSINESS POLITICS)
Firaministan Spain Mariano RajoyHoto: Reuters

Firaministan Spain Mariano Rajoy ya bayyana wa majalisar dokokin ƙasar sa jerin sabbin matakan tsuke bakin aljihun da gwamnatin sa ke shirin aiwatar wa. Daga cikin matakan dai harda ƙarin kaso ukku cikin 100 akan harajin da gwamnati ke karɓa wanda a yanzu ya kai na kashi 21 cikin 100, kana da rage yawan kuɗaɗen da gwamnati ke kashewa da ƙarin Euro miliyan dubu ukku da dubu 500 ta hanyar soke alawus-alawus na kirsimeti ga ma'aikatan gwamnati kana da ragin kuɗin haraji ga waɗanda ke sayan gidaje.

Hakanan firaministan na Spain ya bayyana rage kuɗaɗen tallafin da hukumomi ke baiwa marasa aikin yi da kuma na jami'an ƙananan hukumomi. Firaminista Rajoy ya sanar da majalisar dokokin Spain cewar, ƙasar na fama da matsalar koma bayan tattalin arziƙi mafi muni a cikin tarihin ta, yana mai cewar matsalar za ta ci gaba har ya zuwa aƙalla shekara guda nan gaba.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou