1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin matakan warware rikicin Siriya

April 21, 2012

Majalisar Ɗinkin Duniya za ta amince da wani sabon ƙudirin ƙara yawan masu sanya ido akan tsagaita wuta a Siriya.

Member states vote on a draft resolution backing an Arab League call for Syrian President Bashar Assad to step down, which was later vetoed by Russia and China, during a meeting of the United Nations Security Council at UN headquarters Saturday, Feb. 4, 2012. The unusual weekend session comes as Syrian forces pummel the city of Homs with mortars and artillery in what activists are calling one of the bloodiest episodes of the uprising. (AP Photo/Jason DeCrow)
Zaman kwamitin sulhun MƊDHoto: dapd

A wannan Asabar ce kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ke jefa ƙuri'ar amincewa da wani sabon ƙudirin daya tanadi baiwa mambobi 300 na rundunar da za ta tura damar sanya ido akan yarjejeniyar tsagaita buɗe wuta a Siriya. A wannan makon ne sakatare janar na Majalisar Ɗinkin Duniya Ban Ki Moon ya buƙaci ƙara yawan mambobin rundunar duk kuwa da cewar ya bayyana cewar shugaba Bashar al-Assad bai mutunta alƙawarin daya ɗauka na janyo dakaru da kuma manyan bindigogi daga manyan biranen ƙasar ba.

Tunda farko dai jami'an ƙungiyar tarayyar Turai sun yi barazanar ƙara sanyawa Siriyar takunkumi muddin dai ba ta kyale sauran mambobin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Ɗinkin Duniya suka shiga cikin ƙasar ba. Ya zuwa yanzu wakilan Majalisar bakwai ne kachal ke Siriyar, a dai dai lokacin da Majalisar Ɗinkin Duniyar ta amince da tura wakilai kimanin 30 domin sanya ido akan yarjejeniyar tsagaita buɗe wutar a makon gobe, kana da wasu 300 a nan gaba.

A ranar 12 ga watan Afrilun nan ne aka fara yin aiki da wani ƙudirin Majalisar Ɗinkin Duniya game da tsagaita wuta a ƙasar ta Siriya domin kawo ƙarshen rikicin ƙasar daya zuwa yanzu ya janyo mutuwar fiye da mutane dubu 11 a tsawon kimanin watanni 13n da aka yi ana tafka rikicin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Zainab Mohammed Abubakar