1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin sojojin Ukraine na horo mai hadari

August 4, 2023

Yayin da ake ci gaba da yaki a Ukraine, 'yan kasar kalilan ne ke yin rejista don gudanar da aikin sa kai na soja. Horon da ake yi wa sabbin daukan na da tsanani, yayin da ayyukansu ke gudana a wurare masu hadari.

Sojojin Ukraine na samun horo daga kasashe da dama na TuraiHoto: Kin Cheung/AP/picture alliance

 

Masu sha'awar koyon aikin soji da ke da muradin yi wa Ukraine aiki na rige-rigen koyon duk wani abu da ake nuna musu. Ana shafe sama da wata daya ana horar da su, kuma yanzu abin da ke gabansu shi ne koyon yadda za su far ma abokan gaba. Wasu daga cikin jami'ai irin Nightingale kamar yadda ake kiransa, makwanni kadan suka shafe na horo. Ya ce: "Akwai dalilin da suka sa sojoji ba sa horon wata biyu, muna bukatar Karin horo. Sai dai muna cikin wani yanayi da abubuwa suka rincabe."

Yaki ya sa Ukraine diban sabbin sojoji tare da horas da suHoto: DW

Kutsawa domin samar da hanya ba abu ne mai muhimmanci kadai ba, amma mai hadari. Abin da sojojin ke gani a matsayin jan aiki a gabansu shi ne atisayen farko, wanda idan har aka yi nasara, sauran na zuwa da sauki. Nightingale ya ce: "Ina kan gaba kuma mun tarwatsa mabuyar makiya a wani waje, abun tsoro ne. Za ka yi ta kokarin buya cikin bishiyoyi a daidai lokacin da ake ta zazzaga ma ruwan wuta".

Babu wata kididdiga a hukumance da ke nuna adadin sojoji da suke mutuwa yayin yakin Ukraine. Amma da yawa sun rigamu gidan gaskiya idan aka yi la'akari da yawan sabbin masu aikin sa kai na soja da ake dauka. Tawagar kwararrun sojojin da matasa ke aiki da su ba ta da nisa daga inda ake atisayen, inda ba ta fi kilomita 20 da birnin Bakhmut ba. Sojoji na gwabzawa kuma wasu daga cikin masu horar da sabbin diba na kasancewa kwararrun sojoji ne da aka zakulo daga fagen daga, kuma ana sauyawa daga lokaci zuwa lokaci.

Masu aikin sa kai na soja na samun gejeren horo a UkraineHoto: OLEG PALCHYK/Territorial Defence Forces of Ukraine

Pharaoh da ke zama daya daga cikin kwamnadojin sojin Ukraine da ke horas da wadannan mutane ya ce: ." Shakka babu akwai bambanci tsakanin sabbin shiga da kuma wadanda suka shafe shekara biyar ko shida ko ma uku suna aiki. Bana ganin cewa akwai nakasu kan yadda horon ke gudana, a yanzu muna da kwararrun kwamandoji wadanda za su horar da su sosai."

Wadannan mutanen da ke sa ran zama sabbin sojojin Ukraine suna amsa kira a yayin atisaye, ko da kuwa sun kasance a cikin hutu.