1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabbin jiragen fatattakar 'yan ta'adda a Najeriya

Uwais Abubakar Idris AMA
July 23, 2021

Gwamnatin Najeriya ta karbi jiragen saman yaki samfarin Super Tucano da ta cefano daga Amirka, a kokarinta na kara kaimi wajen yaki da 'yan bindiga da masu aiyyukan ta’adanci.

Waffen Handel von Angola Kriegsflugzeug Flugzeug Super Tucano
Super Tucano irin samfarin jiragen da Najeriya ta sayo daga AmirkaHoto: Embraer

Jiragen sama yakin samfurin Super Tucano guda shida ne suka iso a Najeriya, abinda ya kawo karshen dogon jira da rashin tabbas a Najeriya na fiye da shekaru uku bayan da kasar ta sanya hannu a kan yarjejeniya da Amirika don sawo wadannan jiragen saman yaki na zamani a kasar da ke fama da munanan matsaloli na rashin tsaro da aiyyukan ta’adanci. Ko mene ne muhimmancin kaiwa ga wannan mataki da Najeriyar ta dade tana kwadayin samu a yakin da take da ta’adanci? Captain Yahya J Umar Damagum mai ritaya kwararren sojan sama ne kuma masani a fanin tsaro ne ya ce "Jirgin sama a fagen yaki abu ne mai taimakawa, saboda duk yawancin yakin da aka yi jirgi ya taimaka sosai, haka kuma kasashen da ke da karfin makamai, suna yawan amfani da jirage, kamar yadda hakan ya kasance a yankin duniya na biyu. Samun jirage na tabbatar da cewa kuna da kayan yaki a cikin tafiyar."

Karin Bayani: Arewacin Najeriya a cikin matsalar tsaro

Sojan Najeriya na yaki da Boko HaramHoto: picture-alliance/dpa

Jirgin saman yaki na Super Tucano dai na da wasu kebantattun abubuwa a kan sauran ire-irensa, domin bayanai sun nuna yadda yake da inganci wajen aikin tattaro bayanan sirri a kan maboyar abokan gaba, ga hanzari wajen kai dauki ga sojojin da ke yaki a kasa a fagen daga, abinda ya sanya kakakin rundunar sojan saman Najeriya Air Commodore Edward Gabkwet bayyana cewa zai taimaka wajen kai hari ga ‘yan ta’ada da kuma kare farar hula. To sai dai ga Nautura Ashiru Sherrif na hadaddiyar kungiyoyin farar huka a yankin arewacin Najeriya yace ba’a nan take ba, saboda duk da yake abin farin ciki ne samun makamai, yana da kyau a sake salon tafiya."Ya ce abin farin ciki ne da muka jima muna dako dan mun jima muna cewar sojojin Najeriya ba su da kayan yaki, amma yanzu ta wannan jiragen abin jira shi ne a canza salon yakin da ake yi da 'yan ta'adda."

Karin Bayani: Bukatar kafa 'yan sandan jihohi a Najeriya

Rundunar tsaro ta sojan Najeriya tace tuni aka horas da sojojin sama na kasar su 60 yadda zasu sarrafa tare da kulawa da jiragen saman na Super Tucano a Najeriyar, kuma ana ci gaba da horas da sauran kwararru a wannan fani wanda na cikin yarjejeniyar da aka cimawa. Rundunar sojan saman Najeriyar tana fama da yawan faduwar jiragen samanta na yaki, koda a makon jiya sai da masu kai hare-hare a jihar Zamfara suka harbor wani jirgin. Najeriyar na murana da kaiwa ga samun jiragen yaki guda shida na Super Tucano inda za’a kawo mata wasu sauran guda shida nan da karshen shekara, wannan ne dai karon farko a shekaru masu yawa da Amirka ta sayarwa Najeriyar kayan yaki.