1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon ƙuduri kan Siriya

September 28, 2011

Ƙasashen Birtaniya da Faransa da Jamus da Portugal sun gabatar da sabon ƙuduri da ya buƙaci dakarun Siriya su daina ɗaukar matakan murƙushe boren nuna adawa da gwamnati

'Yan boren ƙin jinin gwamnatin SiriyaHoto: dapd

A cikin wani ƙuduri da suka gabatar a gaban komitin sulhu na Majalisar Ɗinkin Duniya ƙasahen Birtaniya da Faransa da Jamus da Portugal tare da goyon bayan Amirka su yi kira ga komitin da ya yi Allah wadai da ci-gaba da ɗaukar matakan murƙushe zanga-zangar nuna adawa da gwamnati a Siriya . To sai dai ƙudurin bai ƙunshe da buƙatar ƙaƙaba takunkumi da yake ƙasashen Rasha da China sun yi barazanar hawa kujera game da wannan bukata. To amma ƙudurin ya yi barazanar ƙaƙaba takunkumi in har aka ci gaba da ɗaukar matakin ba sani ba sabo akan 'yan zanga-zangar.

Tun daga watan Maris ne dai dakarun gwamnatin Siriya ke ɗaukar matakan murƙushe wannan bore. A ma wani rikici da aka fuskanta a baya bayan sai da dakarun suka yi amfani da tankoki wajen auka wa garin Rastan da ke zama mafaka ga sojojin da suka yi canjin sheka.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Usman Shehu Usman