1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Startschuss für ESM

October 8, 2012

Ministocin kasashe 17 da ke amfani da kudin Euro za su girka asusun ceto kudin Euro Wato ESM.

EU Euro Wahrung Logo ESM. http://www.efsf.europa.eu/attachments/fi/esm_investor_presentation.pdf

A zaman da za su yi a Luxembourg ministan kudin Jamus, Wolfgang Schaueble da sauran takwarorinsa za su rattaba hannu kan wasu takaradu na wannan shiri. Shi dai wannan asusu na ESM wanda nan da wasu 'yan watanni zai samar da Euro miliyan dubu 700 ko da yake zai maye gurbin tsohon asusun EFSF to amma har yanzu zai ci gaba da kasancewa karkashin inuwarsa. Kafin watan Satumban shekarar 2013 ne kuma ake sa ran ma'aikatan tsohon asusun su 40 za su gina wannan sabon asusun na dindindin da zai ba da kariya ga kasashen masu amfani da Euro da ke fama da karayar tattalin arziki. Klaus Regling, shugaban tsohon asusun EFSF wanda shi ne kuma ne zai jagoranci sabon asusun ya bayyana shirin da aka yi domin girka asusun. Ya ce:

" Mu yi shiri sosai wajen girka wannan asusu da ke zaman asusu na dindindin ta yadda zai iya yin aiki a matsayinsa na tsarin da zai tabbatar da dorewar kudin Euro tun daga ranar kafuwarsa. Alal misali ma'aikatan tsohon asusun za su yi aiki tare da sabon har ya zuwa lokacin da aiki zai kammala a cikin tsanaki.

Regling ya kuma ba da sanarwar matakin gabatar da wannan asusun ga masu zuba jari daga kasuwannin duniya.

"Za mu gabatar da wannan asusu ga masu zuba a fadin duniya domin mu rinka samun labarai game da wannan asusu a matsayinsa na sabon shiga a kasuwannin duniya."

Kowace kasa da tata gudunmuwa

Su dai kasashe 17 da ke amfani da kudin Euro za su ba da tsabar kudi na Euro miliyan dubu 80 ga wannan asusu. Akwai kuma Euro miliyan dubu 620 da aka yi alkawarin ba da su da ake ganin za su bai wa asusun damar sayen hannayen basuka a kasuwannin hada-hadar kudi. Kuma ribar da za a samu daga wadannan kudade za a yi amfani da ita wajen tallafa wa kasashe. To sai dai a hakika daga Euro miliyan dubu bakwai da asusun zai kunsa miliyan dubu biyar ne kadai za a ba da su a matsayin rance . sauran kuma za a ajiye su ne a matsayin tabbaci ga masu zuba jari a cikin asusun. Kasar Jamus ita ce ke gaba da gudunmuwar kusan kashi 27 daga dari na asusun da kotun tsarin mulkin kasar dake a birnin Kalsruhe ta amince da ba da su. Sai kuma Faransa da Italiya dake biye.

Zaman majalisar dokokin Bundestag akan ESMHoto: Reuters

Jamus za ta ba da kaso babba

Ga ministan kudin Jamus Wolfgagang Schaueble dai kashi 27 daga cikin dari na euro miliyan dubu bakwan da ya kama euro miliyan dubu 190 da majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta sa hannu akai na a matsasyin babbar gudunmuwa ta Jamus. Shi dai Wolfgang Schauble shi ne ke wakiltar Jamus a komitin da ke kula da asusun inda shi da sauran ministocin kudin kasashe 16 za su tsai da shawara akan kasashen da ya kamata a ba wa tallafi, da kudin da za a bayar a matsayin tallafi da kuma sharuddan ba da tallafin. Schaueble ya ce:

Wolfgang Schauble, ministan kudin JamusHoto: Reuters

" Hakan bai saba wa doka ba. Kuma amincewa da hakan da kotun tsarin mulki ta yi ya yi daidai. Aluma kuma a yanzu sun yi amanna da haka."

Kasar Spain ita ce za ta fara cin gajayar wannan asusun kasancewar tuni gwamnatinta ta ba da sanarwar cewa za ta mika takardar neman Euro miliyan dubu 40 domin ta da komadar bankunanta da suka yi kasa a gwiwa.

Shi dai Hans-Werner Sinn shugaban cibiyar binciken tattalin arziki dake a birnin Munich a cikin hirar da wani gidan telebijan yayi da shi ya yi kashedin cewa wannan asusun bai zaman mafita daga matsalar bashi da ke addabar kasashen Turai.

Za ku iya sauraron sautin wannan rahoto daga kasa.

Mawallafi: Berndt Riegert/Halima Balaraba Abbas
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe