Sabon fada ya barke a Sudan ta Kudu
October 29, 2014Talla
An yi kazamin dauki ba dadi tsakanin sojojin kasar Sudan ta Kudu da mayakan 'yan tawaye a garin Bentiu mai arzikin man fetur, domin kwace garin daga hannun dakarun gwamnatin. Sojoji da ma'aikatan agaji sun tabbatar da faruwar lamarin. Wani kakakin soji ya ce an kai hare-hare daga kudanci da arewacin birnin.
Sabon fadan ya kawo karshen tsagaita wutar da aka samu tsakanin bangarorin biyu na Shugaba Salva Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar. Duk bangarorin na kasar Sudan ta Kudu suna karkashin matsin lamba na cimma yarjejeniyar tsagaita wuta, tun bayan barkewar rikici a watan Disamba.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe