Sabon Firaministan Spain, Zapatero yayi alkawarin janye dakarun kasar daga Iraki.
March 15, 2004Kamar sauran jama´a a kasar Spain, a cikin sharhin da ta rubuta jaridar El Mundo mai ra´ayin mazan jiya ta kwatanta nasarar da jam´iyar ´yan socialist ta samu da cewa wani lada ne bisa kwarjinin Zapatero sannan a hannu daya kuma wani jan kunne ne ga jam´iyar People´s Party.
Ko shakka babu hare-haren da aka kaiwa birnin Madrid da kuma abubuwan da suka biyo baya sun taka muhimmiyar rawa ga wannan nasara ta jam´iyar ´yan socialist, domin al´umar wannan kasa sun dade suna korafin cewa gwamnati na yaudarar su. Kuma duk da cewa daga baya duk duniya ta san babu hannun kungiyar ETA a wannan hare-haren, amma gwamnati ta hakikance cewar wannan kungiya ce ta aikata wannan danyan aiki.
Saboda irin wannan manufar ta farfaganda da jam´iyar people´s party ta masu ra´ayin mazan jiya ta dade tana bi, ya sa a wannan lokaci masu jefa kuri´a suka juya mata baya. A daura da haka, FM mai jiran gado karkashin gwamnatin jam´iyar ´yan socialist Jose Luis Rodriguez Zapatero yayi wa al´umar kasar alkawarin canza manufofin gwamnati.
A wani lokaci yau din nan sabon FM zai gana da sauran jam´iyun siyasar kasar, inda zasu tattauna game da wasu muhimman batutuwa kamar yaki da ´yan ta´adda a Spain. A dai halin da ake ciki ana ci-gaba da neman wadanda ke da hannu a harin ta´addancin na ranar alhamis. Jaridar kasar da ake kira El Pais ta ce daya daga cikin ´yan kasar Marokko da aka kama a ranar asabar yana da hannu dumu dumu a hare-haren na rana 11 ga wannan wata na maris. Bugu da kari ana zarginsa da zama dan bangaren kungiyar al-Qaida a Spain da kuma Marokko. Watakila ma yana da hannu a hare-haren da aka kaiwa birnin Kasablanka. Yayin da ake karfafa zaton cewa kungiyar al-Qaida ta kai wadannan hare-haren, su kuwa al´umar Spain na kara zargin gwamnatin Jose Maria Aznar ne da janyo musu wannan bala´i sakamakon manufofin ta game da Iraki. Daukacin al´umar wannan kasa dai sun nuna adawa da yakin na Iraki, amma FM Aznar yayi amfani da rinjaye sa a majalisar dokoki don samun goyon bayan tura dakarun kasar zuwa Iraki.
Saboda haka sabon FM Zapatero bai yi wata ba wajen jaddada alkwarin da ya dauka tun lokacin yakin nema zabe cewa zai janye dakarun Spain daga Iraki, idan MDD ba ta karbi ragamar wannan kasa zuwa 30 ga watan yuni ba. Ko da yake fargabar sake kaiwa kasar hare-haren ta´addanci da kuma sabuwar alkiblar game da manufofinta na Iraki sune suka mamaye zukatan mutane, amma daukacin mutane na tune da cewa gwamnati zata fuskanci kalubale na tattalin arziki. Domin tsohuwar gwamnatin ´yan socialist da ta taba jan ragamar mulki, ta tafi ta bar kasar da matsalolin tattalin arziki, saboda haka wasu ´yan kasar ke nuna damuwa game da wannan canjin gwamnati da aka samu.