1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon hari a kudancin Kordafan na Sudan

June 14, 2013

An kai hari a kudancin Kordafan na Sudan, inda sabon hari da aka kai ya yi sanadiyyar mutuwar jami'in wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.

epa02750699 A photograph released by the United Nations Mission in Sudan (UNMIS) on 25 May, shows the arrival of the first of 125 Indian Force Reserve Battalion troops in the town of Abyei, Sudan, 24 May 2011. The reserve company was dispatched to Abyei, the town that straddles the border between North and South Sudan and had been seized by government troops from Khartoum on 22 May 2011, to prevent renewed looting and burning of properties which had erupted after the takeover. Abyei's political status has remained undecided after South Sudan in January voted to secede. EPA/STUART PRICE / HANDOUT HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES +++(c) dpa - Bildfunk+++
Wani sojan MDD a SudanHoto: picture-alliance/dpa

Wasu tagwayen harbe-harbe da bingogi sun fada kan sansanin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Sudan, inda suka yi sanadiyyar mutuwar wani jami'in wanzar da zaman lafiya guda.

Rahotanni sun bayyana cewa harbe-harben da suka fada kan sansanin dakarun wanzar da zaman lafiyar na Majalisar Dinkin Duniya da ke garin Kadugli a kudancin Kordafan. a wannan yankin dai ana ci gaba da samun rikici tsakanin gwamnatin Sudan da kuma 'yan tawaye a tsahon shekaru biyun da suka gabata, kuma ana kyauta zaton cewa sune suka yi sanadiyyar mutuwar jami'in.

Kasar Sudan dai na zargin makwabciyarta Sudan ta Kudu da marawa 'yan tawayen na kudancin Kordafan baya, zargin da Juba ke ci gaba da musantawa.

Ya zuwa yanzu dai Majalisar Dinkin Duniyar ta ce ba za ta iya cewa ga wadanda suka kai harin ba, inda kakakin rundunar wanzar da zaman lafiyar Kieran Dwyer, da ya tabbatar da harin ya bayyana wa manema labarai cewa sun yi Allah wadai da shi.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Usman Shehu Usman