1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bam ya tashi a Somaliya

Abdul-raheem Hassan
March 29, 2021

Akalla mutane hudu sun mutu wasu sun jikkata a wani sabon harin bam da ya tashi a gefen titi a Mogadishu babban birnin kasar Somaliya, wani jami'in gwamnati ya sha dakyar a harin.

Somalia Selbstmord-Bombe in Mogadischu
Hoto: Farah Abdi Warsameh/AP Photo/picture alliance

Wani jami'ain gwamnati ya ce shi aka danawa bam din amma ya tsallake rijiya da baya, daga bisani harin ya ritsa da 'yan kasuwa a gefen titi. Wata mata da jariri na cikin wadandan da suka mutu nan take bayan tashin bam din.

Birnin Mogadishu ya dade yana fuskantar farmakin 'yan tada kayar baya na kungiyar al-Shabab wadanda suka sha alwashin kifar da gwamnatin Somaliya, inda ko a watan jiya sai da wani hari ya yi sanadiyar mutane 10 a wani gidan cin abinci.