1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kai wa dakarun Mali hari

Abdul-raheem Hassan
March 2, 2020

Rundunar sojin kasar Mali ta tabbatar da mutuwar dakarunta shida wasu akalla 10 sun jikkata a wani sabon harin da aka kai da rokoki a shingen binciken sojojin.

Mali Bundeswehrsoldat mit Sturmgewehr G36 (picture-alliance/dpa/M. Kappeler )
Hoto: picture alliance/dpa

Sojojin gwamnatin Mali sun ce harin ya lalata kayayyaki da motoci da dama daga bangarensu, yayin da su kuma suka yi ikirarin lalata ababaen hawan mayakan.

Mazauana yankin Mandoro da ke kan iyaka da kasar Burkina Faso inda aka kashe sojoji 40 a watan Satumba 2019, na fargabar sojoji za su iya janyewa daga yankin.