Harin bam ya kashe mutane Somaliya
December 28, 2019Talla
Alkaluman baya-bayannan na cewa kusan mutane 90 ne suka mutu sama da mutane 50 sun jikkata a sabon harin bam da bata gari suka kaddamar a lokacin da ma'aikata da sauran jama'a ke zirga-zirga a Mogadishu babban birnin kasar.
Gwamnatin Somaliya ta ce wannan hari na cikin hare-hare mafi muni da kasar ta fuskanta a shekarun baya-bayannan. Babu kungiyar da suka dauki alhakin harin nan take, amma kungiyar al-Shabaab mai alaka da al-Qaida ta sha kai makamancin wannan hari a ciki da wajen kasar ta Somaliya.