Sabon harin ta'addanci a Mali
March 6, 2017Talla
Kakakin ma'aikatar harkokin kasashen ketaren Malin wanda ya tabbatar da afkuwar harin ya nunar da cewa tuni aka kara yawan jami'an tsaro a wajen, sai dai bai yi karin haske kan ko an kama maharan ba ko kuma sun tsere. Kawo yanzu dai babu wani ko wata kungiya da ta dauki nauyin kai wannan harin, sai dai a watannin baya-bayan nan masu kaifin kishin addini da suka hadar da kungiyoyin da ke da alaka da al-Qaeda sun kai hare-hare kan sojojin kasar ta Mali, kana kungiyar 'yan ta'addan Ansar ma ta kai hare-hare masu yawa a kan jami'an Majalisar Dinkin Duniya da sauran yankuna a kasar, a kokarin da take na yada abin da ta kira da Jihadi a yankunan da masu sanya idanu na kasa da kasa suka bayyana da cewa basu da hadari a kasar.