Kamaru: Tsugune ta gaza karewa
May 17, 2019Wannan harin na 'yan awaren ya zo ne bayan da wasu matasa suka mika wuya da gwamnati ta bayyana cewa 'yan awaren ne, sai dai babu tabbacin wadannan matasan na daga cikin masu fafutukar kafa kasarsu mai cin gashin kanta. An dai kai harin ne yayin da Firaminista Joseph Dion Ngute ke otel dinsa, abin da ya sanya shi dakatar da ziyara a garin Kumba da 'yan awaren suke taka rawar gani musamman tsakain Kumba da Buea. Yayin ziyarar ta sa dai Firaminista Dion Ngute ya yi kira ga 'yan awaren da su ajiye makamansu, inda ya ce Shugaba Paul Biya zai zauna kan teburin sulhu domin kawo karshen rikicin kasar da ke neman gagarar kwandila. Sai dai a hannu guda wasu al'ummar kasar na ganin cewa bai kamata a bukaci 'yan aware su ajiye makamaansu yayin da sojojin gwamnati ke rike da nasu ba, kana jagororin 'yan awaren na tsare a gidan kaso abin da ke sanya tunani kan da wa gwamnatin ke shirin tattaunawa tunda ba a sake su ba.