1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Succes Masra jagoran masu neman sauyi a Chadi

Abdourahamane Hassane GAT
August 6, 2019

A kasar Chadi wani matashi mai suna Succès Masra mai ra'ayin neman sauyi ya kafa wata sabuwar kungiyar fafutika mai suna "Transformateur" da nufin samu sauyin shugabanci a kasar. 

Tschad Succès Masra
Hoto: Djérabé Ndingngar

Kasar Chadi na da mahimmanci ga kungiyar Tarrayar Turai, sakamakon yadda shugabanta Idris Deby wanda ke a kan karagar mulki kusan shekaru 38, ke zaman abokin hulda na yaki da ta’addanci da kuma dakile kwararra bakin haure. Sai dai ‚yan kasar ta Chadi na fuskantar galazawa da rashin samun ci gaba da wadata duk da arzikin man fetir da kasar ta mallaka, yayin da yan adawa da kungiyoyin farar fula ake murkushe su. Amma kuma duk da haka kasashen Turan ba su damu ba, cikin irin wannan yanayin ne aka samu wani matashin Succès Masra tsohon ma’aikacin Bankin raya kasahen Afirka BAD da yake da manufofin neman sauyi ya kirkiro wani rukunin na masu neman sauyi "Transformateur". Sai dai hukumomin Chadin sun ki amincewa da su a matsayin jamiyyar siyasa. Burinsu dai shi ne a samu sauyin shugabanci a Chadi. 

 Matasa masu akidar siyasa da ake kira da sunan Transformateur masu ra'ayin kawo sauyi na yin amfanin da salon kidan gambara na Rap wajen yin kira ga matasa da su motsa daga barci domin neman canji na shugabannin. Wata budurwa  daya daga cikin wadanda Succes Masra ya janyo hankalinsu a game da halin da kasarsa ta Chadi take ciki ta ce ta gamsu da manufofin matasan:

"Da na hadu da Tranformateur Masra dangane da manufofin da suke da su wanda suka kayatar da ni na yanke shawarar shiga cikin wannan rukunin na masu neman sauyi da ake kira da Farananci Les Transformateurs".



Jagoran masu neman canjin Succes Masra dan kimanin shekaru 35 masani ne na tattalin arziki kana tsohon ma’aikacin Bankin raya kasashen Afirka na BAD wanda ya bar aikinsa na bankin mai albarka domin zuwa rugunmar abin da ya kira ceton kasarsa daga mulkin danniya na Idris Deby wanda ya zo kan karagar mulki kusan shekaru 38 bayan juyin mulki, Masara yakan yin amfanin da kafofin sada zumunta irinsu Facebook domin janyo hankali matasan a game da irin jawaban da yake yi:

Hoto: Getty Images/AFP/L. Marin

'' Mutun na farko da ke aikata ba daidai ba a Chadi shi ne Shugaban Kasar Idriss Deby, dole idan aka ce shugaba na kowa ka dauki alhakin abin da ya biyo baya da ke faruwa, don ba zai iya zama sabanin haka ba.''


A farkon watan Yunin da ya gabata dan gwagwarmayar Succes Masra ya shirya gudanar da wani taro a birnin Ndjamena domin kaddamar da kungiyar masu neman sauyi na rukunin da ake kira Tranformateur, wacce gwamnatin Chadin ta ki amincewa da shi a matsayin jam'iyyar siyasa. A ranar shirya taron 'yan sanda sun yi amfani da hayaki mai sa kwalla da kulake suka tarwatsa su in da ta kai shi jagoran kungiyar Succes Masra kusan sai da ya suma bai ma san cikin halin da ya samu kansa ba:

''Shugaban na Chadi yana cikin hali na dimauta da gigita mi yake jin tsoro, matasansa da ke tasowa wadanda ke da zumudin bauta wa kasarsu, yana jin tsoro sosai har ya canza kundin tsari mulki domin kau da matásan a cikin fafutukar neman mulki ta shugabancin kasar shi da ya zo kusan hekaru 38 a kan mulki yaya ya zo".


Kasar ta Chadi a shekarun baya-bayan nan ta gano karin arzikin man fetir, sai dai duk da haka ci-gaban ta fuskar jin dafin rayuwar al'umma kalilan ne, mutane kishi shida kawai cikin dari ke samun ruwan sha na fonfo da kuma lantarki yayin da kishi 20 cikin dari kawai suka iya karatu da rubu, ga cin hanci da karbar rashawa da ke kara samun gidin zama a kasar. Succes Masra yana cikin aikin canza tunanin al'umma kuma kawo yanzu ya samu magoya baya dubu 100 sannan gargadi jam'an tsaro da ake yin amfanin da su wajen takura wa al'umma:

Hoto: Getty Images/AFP/P. Desmazes


''Ina kira ga masu damara wadanda ake bai wa umarni da su yi harbi a kanmu ko ake iya tambayarsu da su yi haka ya ce ya kamata su yi tunani da makomar 'yayansu, ilimi, kiwon lafiya da sauransu da ma su kansu ta yadda za su samu kyakkyawan albashi kyakkyawar rayuwa.''

Sakon da dan gwagwarmaya Succe Masra yake son ya isa zuwa ga al'ummar Chadi, da wuya ya kai garesu saboda babu wata kafar rediyio ko talabijan da takan iya ba shi dama kana gwamnatin ta haramta yin tarukan jama'a a Chadin a kan hujjar dalilai na tsaro, yayin da kafofin sada zumunta da ke zaman dama ta karshe a gareshi ita ma take da cikas sakamakon yadda gwamnatin ta Chadi ta dauki matakin cire hanoyoyin sadarwar na intanet wanda ba kowa ba yake da sukunin samu ba.