1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ta'addanciNijar

Sabon kawancen tsaro na Sahel zai fuskanci kalubale

September 19, 2023

Kungiyar G5 Sahel ta shafe shekaru tana yaki da masu tsattsauran ra'ayi a yankin. Amma wasu masana na kallon sabon kawancen da kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar suka kafa na iya mayar da nakasu ga yunkurin Faransa.

 Assimi Goïta da Abdourahamane Tiani da Ibrahim Traoré
Assimi Goïta da Abdourahamane Tiani da Ibrahim Traoré Hoto: Francis Kokoroko/REUTERS; ORTN - Télé Sahel/AFP/Getty; Mikhail Metzel/TASS/picture alliance

Matakin da jagororin juyin mulkin sojan Mali da Burkina Faso da Nijar suka yanke na ficewa daga kungiyar G5 Sahel da Faransa ta taimaka aka kafa na iya kawo karshenta, kamar yadda wasu masana suka bayyana. Shugaban mulkin soja na kasar Mali Assimi Goita ya ce sabuwar kungiyar hadin kan yankin Sahel za ta kafa sabon tubalin tsaro na hadin gwiwa da taimakon juna.

Mutaru Mumuni Muktar, babban darektan cibiyar yaki da tsattsauran ra'ayi ta yammacin Afirka ya jaddada cewa an dade ana sa ran ballewar Mali da Burkina Faso da Nijar, saboda "a cikin dukkanin kasashe uku, akwai kyamar Faransa da ke ci- gaba. Kuma a halin yanzu, akwai muhimmin yunkurin da ake yi don fitar da dakarun G5  ko mayar da su saniyar ware."

Karin bayani:Kokarin dakile ta'addanci a yankin Sahel 

Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye DiopHoto: Yuri Kadobnov/REUTERS

Kasashen Chadi da Moritaniya da ke da wakilci a kungiyar G5 Sahel ba sa cikin sabon kawancen da aka sanya wa hannu a Bamako babban birnin Mali. Ministan harkokin wajen Mali Abdoulaye Diop ya shaida wa manema labarai cewar, "wannan kawancen zai kasance hadin gambiza ne na aikin tsaro da na tattalin arziki tsakanin kasashen uku, amma za a ba da fifiko kan yakar ta'addanc i a dukkan kasashen uku."

Tabarbarewar harkokin tsaro a yankin Sahel

Yankin Sahel na fama da tashe-tashen hankula tun shekarar 2014, inda tashin hankalin kan fararen hula ya haifar da matsalar jin kai wanda ta jefa sama da mutane miliyan 24 cikin bukatar agaji. Sannan mutane miliyan 4.9 sun rasa matsugunansu sakamakon rikici a yankin da ke hada iyakokin Burkina Faso da Mali da Nijar. Amma dai Majalisar Dinkin Duniya ta jaddada bukatar karfafa goyon baya tare da tsaurara yaki da ta'addanci.

karin bayaniSahel: Ingantuwar hadin kai a yaki da ta'addanci

Shekaru tara sojojin Sahel suka shafe suna yakar ta'addanci a yankinHoto: Hans Lucas/IMAGO

Bram Posthumus da ke zama masani a yankin Sahel ya shaidawa DW cewa tun bayan da sojoji suka karbi ragamar mulki a kasashen Mali da Burkina Faso da Nijar, lamarin tsaro ya kara tabarbarewa a kasashen. Ya ce: "Juyin mulki bai kawo  kwanciyar hankali ba, maimakon haka ya kawo rashin zaman lafiya. Kuma sun bai wa abokan gaba da kungiyoyin da ke dauke da makamai damar kara tasirinsu a yankunan da suke iko da su. Don haka babu wani ci-gaba da aka samu a fannin tsaro a yankin Sahel bayan juyin mulkin, akasin haka ne ya faru inda aka samu tabarbarewar tsaro."

Amma gwamnatocin mulkin sojan a kasashen uku sun yi imanin cewa suna da hanyoyin magance matsalar ta tsaro tare da tsara wata sabuwar hanyar kyautata makomar kasashensu. Amma dan jarida Seidick Abba ya nuna shakku game da samun ci-gaba sakamakon rashin damawa da Chadi da Moritaniya. Ya ce ya kamata Nijar ta cimma wata yarjejeniya da makwabtanta: " Yana da kyau Nijar ta samu dabarun yaki da ta'addanci tare da kasar Chadi, tunda ita ma Nijar na fuskantar kalubalen Boko Haram."