1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon kudirin kwamitin sulhun MDD akan Siriya

April 14, 2012

Kwamitin sulhun Majalisar Dinkin Duniya ya sami goyon bayan daukacin mambobinsa wajen tura tawagar soji domin sanya ido akan tsagaita wuta a Siriya

U.S. ambassador to the United Nations Susan Rice speaks to the media about issues in Syria, North Korea and Guinea Bissau after Security Council consultations at the United Nations in New York April 13, 2012. The U.N. Security Council "deplored" on Friday North Korea's failed bid to launch a long-range rocket but said it would continue talks on an appropriate response to the actions of the hermit state, Susan Rice said. REUTERS/Allison Joyce (UNITED STATES - Tags: POLITICS)
Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan RiceHoto: Reuters

Kasashen Rasha da China sun bi sahun sauran takwarorinsu da ke kwamitin sulhu wajen amincewa da tura wata tawagar soji mai mambobin 30 domin sanya ido kan matakin tsagaita wutar da ta fara aiki a Siriya tun ranar alhamis, wanda kuma wakilin alummar kasa da kasa a rikicin Siriyar Kofi Annan ya nema. Wannan ne karon farko da kwamitin mai mambobi 15 ke amincewa da wani kuduri dangane da rikicin siriyar tun bayan kaddamar da rikicin na tsawon watanni 13 yanzu. Sau biyu mahukuntan Moscow da Beijing ke darewa kan kujerar naki dangane da kudurin kwamitin sulhun, kuma Rasha ta yi gargadin cewa akwai matsayin da majalisar ba zata iya kurewa ba a irin matakan da zata dauka kan Siriyar. Jakadar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya Susan Rice ce ta gabatar da sakamakon zaben

"Ga kuma yadda sakamakon zaben ya kasance, kuri'u goma sha biyar suka goyi bayan daftarin kudurin, kudurin bai sami hammaya ba, dan haka an amince da shi a matsayin kuduri mai lamba dubu biyu da arba'in da biyu na shekarar dubu biyu da goma sha biyu"

Wannan kuduri ya tanadi bangarorin gwamnati da na adawa su tsagaita wuta kuma yayi gargadin cewa kwamitin Sulhun da kan shi ne zai aiwatar da tanadin kudurin, ya kuma yanke hukunci dangane da irin abubuwan da suka bayyana.

Mawallafiya: Pinado Abdu-Waba
Edita: Saleh Umar Saleh