1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon kudurin Majalisar Dinkin Duniya(MDD) kan Siriya

May 16, 2013

'Yan adawar kasar Siriya sun yi na'am da kudurin majalisar dinkin duniya ta tsayar akan rikicin kasar

)
Hoto: Getty Images

To amma a cikin wani bayani da ya yi kawancen 'yan adawar kasar ta Siriya ya ce Allah wadai da MDD ta yi da gwamnatin kasar bai zai wadatar ba wajen kawo karshen wahalar da yan Siriya ke sha.Ya ce akwai bukatar kara yin matsin lamba ga gwamnatin Bashar al-Assad domin ta ba da damar kai karin taimakon jinkai ga 'yan kasar da ke cikin mawuyacin hali. Bugu da kari kawancen ya mika bukatar shigar da batun hukunta laifukan yaki.

A jiya Laraba ne babbar mashawartar Majalisar Dinkin Duniya ta tsai da kuduri akan yakin basasan kasar ta Siriya tana mai yin kira ga gwamnatin kasar da ta gudanar da sauye-sauyen siyasa. Kasashe mambobi 107 ne dai suka kada kur'iar amincewa da kudurin da kasashen Larabawa suka gabatar, kasashe 59 ne kuma suka kaurace wa kuri'ar. Sai kuma wasu su 12 da suka kada kuri'ar rashin amincewa cikinsu har da Rasha. Shi dai wannan kuduri ya banbanta da na wanda komitin sulhu na MDD ya tsayar da ya bukaci tilasata yin aiki da shi.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Umaru Aliyu