1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Rasha: Sauye-sauye a ma'aikatar tsaro

Lateefa Mustapha Ja'afar
May 20, 2024

Shugaba Vladimir Putin na Rasha ya nada tsohon mataimakin ministan taattalin arzikin kaksar Oleg Savelyev a matsayin sabon mataimakin ministan tsaro.

Rasha | Vladmir Putin | Kwaskwarima | Ma'aikatar Tsaro
Shugaba kasar Rasha Vladmir Putin yayin ziyararsa a ChainaHoto: IMAGO/ITAR-TASS

A makon da ya gabata Shugaba Vladimir Putin na Rashan ya dauki wani mataki da ya bayar da mamaki, inda ya sauke tsohon ministan tsaro Sergei Shoigu tare da maye gurbinsa da Andrei Belousov da ke zaman kwararre a fannin tattalin arziki kana tsohon ministan lura da tattalin arzikin Rashan. Wannan matakin dai na nuni da yadda Putin ke kawo gagarumin sauyi a ma'aikatan tsaron Moscow, wadda ke fama da rikici da ke da nasaba da cin-hanci da rashawa.