Sabon matakin Girka na tsuke bakin aljuhu
June 26, 2011Sabon ministan kuɗin Girka Evangelos Venizelos ya yi kira ga al'umar ƙasarsa da su bayar da haɗin kan da ake bukata ga matakan tsuke bakin aljuhu da gwamanti ta ɗauka domin ceto tattalin arzikin ƙasar da ke cikin mawuyacin hali. Venizelos ya ce gwamnati ta kwana da sanin cewar matakin na cike da kura-kurai, amma kuma zai hana ƙasar ta girka faɗawa cikin koma bayan tattalin arziki.
Majalisar dokokin ƙasar na shirin kaɗa ƙuri'ar domin amincewa koko akasin haka da sabon matakn tsuke bakin aljuhu da gwamnati ta ɗauka. Wannan mataki zai bai wa ƙasar ta Girka damar samun ƙarin tallafi daga ƙungiyar Tarayyar Turai da kuma asusun bayar da lamuni na duniya.
ƙungiyoyin ƙodagon ƙasar sun yi kira da a gudanar da yajin aikin gama gari a ranakun talata da kuma laraba domin nuna rashin jin daɗi da matakin tsuke bakin alhuju da gwamanti ta ɗauka.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Umaru Aliyu