1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Yaushe za a shawo kan rashin tsaro?

March 27, 2026

Kwanaki kadan bayan taron hadin gwiwa tsakanin Benin da Code d'ivoire da kuma Faransa wanda akayi a Cotonou domin dakile matsalar tsaro, babban hafsan sojojin kasa Janar Mamane Sani Kiaou ya kai ziyarar aiki Gaya.

Nijar | Shugaba | Mulkin Soja | Janar Abdourahamane Tiani
Shugaban gwamnatin mulkin soja ta Nijar Janar Abdourahamane TianiHoto: AFP/Getty Images

A ziyarar da ya kai babban hasfan runduwar sojojin kasa Janar Mamane Sani Kiaou ya mayar da hankali kan wani katafaren filin gina barikin soja na zamanin, daga bisani ya ziyarci rundunar tsaro ta soja da aka girke a gadar Gaya–Malanville. Wannan na zuwa ne mako guda da taron hadin gwiwar Benin da Code d'ivoire da kuma Faransa. Sai dai a cewar Haruna Hanci dan asalin yankin na Gaya, wannan ziyar ta kwantar musu da hankali.

Ziyarar bayar da kwarin gwiwa?

Ficewar Nijar daga rundunar tsaron MNJTF

03:40

This browser does not support the video element.

Ziyarar dai tamkar jefa tsuntu biyu ne da ductse guda, a cewar Souley Oumarou Madugun farar hula masu fafutukar kare hakkin dan Adam da kuma tabbatar da kyakkyawan shugabanci. Baya ga Gaya Janar Kiaou ya wuce garin tanda mai nisan kilomita 20 da garin na Gaya da shi ma ke fama da matsalolin tsaro, inda a can ma ya jinjinawa sojojin da suke aiki a yankin. Daga nan kuma ya wuce yankin Boumba, tare da tattaunawa da rundunar tsaron yankin.

Kokarin dakile matsalar tsaro

Nijar: Matsalar tsaro ta shafi ilimi

04:01

This browser does not support the video element.

A cewar Moussa Modibbo wani mai nazari kan harkokin yau da kullum, wannan ziyarar za ta dada karfafa gwiwar sojojin da suke a bakin daga a kan iyar Gaya da Benin. Sai dai a cewar Alfa Moussa ya kamata sojojin su hada kai da al'umma, domin hakan zai iya dakile matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin. Kawo yanzu dai an kara karfafa matakan tsaro a kan iyakar Nijar da Benin, ta hanyar baza sojojin wadanda suke cikin shirin ko-ta-kwana.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani