1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon matsayin Turai akan rikicin Siriya

August 30, 2011

Turai ta bayyana sanya takunkumin shigowa da mai daga Siriya, tare da bayyana ƙudirin ɗaukan wasu matakai

Kantomar kula da manufofin ƙetare na Turai Catherine AshtonHoto: AP

Jami'an diflomasiyyar ƙungiyar tarayar Turai sun sanar da cewar, ƙungiyar ta amince ta sanya sabbin takunkumi akan kamfanonin ƙasar Siriya da kuma hana shigowa Turai da man fetur daga ƙasar ta Siriya. Hakanan kuma a wannan Talatar ce ƙungiyar - mai ƙasashe mambobi 27 ke gudanar da sabuwar tattaunawar duba yiwuwar faɗaɗa takunkumin akan shugaban Siriya Bashar al-Assad. Manufar hakan dai ita ce ƙara matsin lamba akan shugaba Assad ya dakatar da tsauraran matakan da gwamnatin sa ke ɗauka a ƙoƙarin da take yi na daƙile masu boren adawa da ita. Tuni dama ƙungiyar ta sanya takunkumin hana tafiye-tafiye da kuma taɓa dukiya akan shugaban na Siriya da kuma muƙarraban sa. Tarayyar Turai ce dai ke sahun farko wajen shigo da man fetur daga ƙasar Siriya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu