Sabon rahoton hukumar IAEA kan shirin nukiliyar Iran
November 16, 2007Talla
Ƙakashe da dama sun mayar da martani daban daban a kan sabon rahoton da hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa IAEA ta bayar game da shirin nukiliyar nukiliyar Iran da ake takaddama a kai. Ƙasashen Amirka da Birtaniya sun sanar da cewa zasu ƙara matsa kaimi wajen faɗaɗa takunkumai akan hukumomin birnin Teheran. Su kuwa a nasu ɓangaren hukumomin na Iran sun ce rahoton na birnin Viennen ya karfafa manufofin su. A cikin rahoton hukumar ta IAEA ta ce Iran ta miƙa gamasassun bayyanai dangane da shirin ta na nukiliya. To sai dai har yanzu tana ci-gaba da yin kunnen uwar shegu ga bukatun MDD na ta daina sarrafa sinadarin uranium.