Sabon rikici a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya
May 30, 2017Wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa sabon rikicin da ya barke a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya yi sanadiyar mutuwar daruruwan mutane, yayin da wasu kimanin 88,000 suka tsere daga gidajensu, tun daga farkon wannan wata na Mayu da muke ciki. Kasar wadda take sahun gaba a cikin kasashen 'yan rabbana ka wadata mu, ta sake samun kanta cikin wannan hali yayin da take kokarin murmurewa daga shekaru uku na yakin basasa tsakanin Musulmi da kungiyar tsageru ta mabiya addinin Kirista.
Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya ya kara da cewa yanzu haka akwai fiye da 'yan gudun hijira a cikin kasar fiye da 500,000, yayin da fiye da 120,000 suka tsere zuwa Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango. Sabon rikicin na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya dai na ritsawa da fararen hula.