1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Sabon rikici a tsakanin Saudiyya da Labanan

Mahmud Yaya Azare MA
November 1, 2021

Masarautar Saudiyya ta sanar da katse huldar diflomasiyya da kasar ta Labanan, matakin da kasashe kawayenta suka bi sawu. Sai dai kasashen Yamma sun ce bai dace ba.

Saudia Arabien Kronprinz Mohammed bin Salman
Hoto: Saudi Royal Court/REUTERS

A karshen mako ne wannan sabuwar dambarwar diflomasiyyar ta taso a tsakanin kasar ta Laebanan a hannu guda da kasashen da ke cikin kawancen da Saudiyya ke jagoranta a yakin Yemen, wato Hadaddiyar Daular Larabawa da Bahrain da Kuwait a daya gefen, bayan da aka yada wani faifayin bidiyo na ministan watsa labaran kasar ta Labanan, George Kordahi, yana sukar Saudiyya da kawayenta kan yakin da take yi a Yemen wata guda kafin a nada shi minista.

Duk da cewa Fira Ministan Labanan Najib Mikati da Shugaban kasar Michel Aoun, sun nesanta kansu da wadannan kalaman da suka ce sun saba wa ra‘ayin gwamnatinsu. Sai dai sun ce ba za su kori ministan kan kalaman da ya yi su kafin ya shigo gwamnati ba, a yayin da shi ma ministan ya sake cewa har yanzu yana nan kan bakarsa kan wannan ra‘ayin nasa, kuma ba shi da aniyar yin murabus don radin kansa.

George Kordahi, Ministan labarai a LabananHoto: Bilal Hussein/AP Photo/picture alliance

Da fari dai an yi zaton wadannan kalaman su ne ummul haba‘isin tunzura Saudiyya da kawayenta na yankin Gulf , har ya kai su ga daukar matakin kira da a sauke ministan, gami da janye jakadansu daga kasar da ma dakatar da duk wasu huldar kasuwanci da ita.

 

Tuni dai ‘yan kasar suka fara gunaguni kan wannan dambarwar diflomasiyyar da suke cewa za ta kara fama ciwon da suke fama da shi ne.

Tuni dai Amirka da Faransa da Jamus suka nuna damuwarsu da janye jakadun Saudiyya da kawayenta daga Labanan, suna masu kira da a mayar da wukar, da kuma cikakken goyon bayansu ga gwamnatin firaim minister Mikati wacce da kyar da jibin goshi a ka yi nasarar kafa ta bayan kwashe shekara guda da watanni ba tare da gwamnati a kasar ba.