SiyasaJamus
Riciki ya barke bayan kafa gwamnati a Isra'ila
June 17, 2021Talla
Kwanaki kalilan bayan kafa sabuwar gwamnatin gamin gambiza a Isra'ila, sabon rikici ya barke tsakanin Faladinawa da Isra'ila, inda jiragen yakinta suka kaddamar da hare-haren ramuwa kan Zirin Gaza, bayan fashewar wasu bala-balan da aka tura daga Zirin Gaza suka jawo tashin gobara a yankunan Isra'ila.