1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Sojojin Azerbaijan sun kai hari Armeniya

Ramatu Garba Baba
September 13, 2022

Rahotanni sun tabbatar da mutuwar sojojin Armeniya akalla 49 a sakamakon hare-haren da sojojin Azerbaijan suka kaddamar kan yankunan kasar a wannan Talata.

Archivbild I Konflikt Berg-Karabach
Hoto: picture alliance/dpa/TASS

Jim kadan da soma kai wa kasar hare-hare, firaiministan kasar Armeniya Nikol Pashinyan ya yi kira ga manyan shugabanin duniya da su gaggauta daukar matakin ladabtar da makwabciyar kasar Azerbaijan a sakamakon kutsa kai da rundunar sojinta suka yi a yankunan kasarsa.

Pashinyan ya sheda wa shugabanin kasashen Faransa da Rasha da kuma sakatare harkokin wajen Amirka ta wayar tarho, irin barazanar da kasar ke ciki a yanzu. Rikicin wadannan kasashen biyu da suka kasance tsoffin kasashen tarayyar Soviet, ya samo asali kan yankin nan na Nagorno-Karabakh da suke jayayya akai duk da cewa an san yankin a matsayin wani bangare na Azerbaijan amma yankin na a karkashin kabilun Armeniya.