Sabon sakataren Majalisar Dinkin duniya ya fara aiki
January 1, 2007Talla
Ban Ki Moon na kasar Koriya ta kudu ya karbi ragamar shugabancin MDD a matsayin sakatar janar na 8.
Dan shekaru 62 Ban ki Moon ya samu nasara ne bisa kann wasu yan takara 6 da suke neman kujerar sakatare janar na MDD.
Ban yace zai yi aiki tukuru wajen samarda karin zaman lafiya a duniya.
A daren jiya ne Kofi Annan ya kammala waadinsa na sakatare janar na MDD bayan shekaru 10.