Sabon sakataren tsaro Amirka ya kai ziyara Bagadaza
December 20, 2006Talla
Kwanaki biyu bayan an rantsad da shi a mukamin sabon sakataren tsaron Amirka Robert Gates ya isa birnin Bagadaza inda zai gana da kwamandojin Amirka tare da ganewa idon sa irin halin da ake ciki a wani yaki da ya ce ya zamewa Amirka alakakai. Ziyarar ta mista Gates mai shekaru 63 ta zo ne bayan wani sabon rahoto da ma´aikatar tsaron Amirka ta bayar cewar tashe tashen hankula a Iraqi ya kazanta fiye da na kowane lokaci. Rahoto ya ce yawan dakarun Amirka da aka kashe a Iraqin yanzu ya kusan dubu 3. A wani labarin kuma fadar White House ta tabbatar da cewa shugaba GWB ya na duba yiwuwar kara yawan dakarun Amirka a Iraqi na wani gajeren lokaci. A wata hira da aka yi da shi Bush ya ce yana shirin fadada rundunar sojin sa don ta samu sukunin tinkarar ayyukan ta´addanci dake dada yin muni a duniya.