Sabon salo na rikicin Sudan da sudan ta Kudu
April 24, 2012Sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da farmaki da Sudan ta kaiwa makwabciyarta Sudan ta Kudu ta sama a yankin Bentiu da kan iyakar ƙasashen biyu. A lokacin da ya ke jawabi ga manaima labarai, kakakin Ban Ki-moon ya ce babban magatakardan ya yi kira ga ƙasashe biyu su kawo ƙarshen kai ruwa rana da suke yi tsakaninsu, wanda kuma zai kai ga haddasa yaƙi tsakanin sudan da kuma jaririyar sudan ta kudu. Su ma dai sauran ƙasshen duniya cki kuwa har da china sun yi nemi ɓangaorin biyu su hau kan teburi tattaunawa domin magance rashin fahimta da ke tsakaninsu.
Sai dai shugaba Omar hasan al-bashir ya yi fatali da duk wani shiri na sansantawa da gwamnatin sudan ta kudu. Maimakaon haka ma dai ya yi barazanar kawar da Salva Kir daga karagar mulkin Sudan ta kudu. A daren litinin zuwa talata ne dai jiragen yakin Sudan suka yi luguden wuta a wata kasuwa da kuma filayen mai a kudancin Sudan, inda mutane aƙalla biyu suka rasa rayukansu. Salva Kiir wanda yanzu haka ya na gudanar da wata ziyarar aiki a China, kasar da shugabanninta suka yi kira ga ɓangarorin biyu da kai hankali nesa.
Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Usma Shehu Usman