1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ondo: Makiyaya su fice daga jiharmu

January 20, 2021

A wani abu da ke zaman alamun sauyin salo a rikicin makiyaya da manoma a Najeriya, ana ka-ce-na-ce tsakanin gwamnatin jihar Ondo da ta nemi makiyaya su bar dazuzzukan jiharta da kuma gwamnatin kasar da ke fadin ba hali.

Nigreria Fulani-Nomaden
Makiyaya na ya da zango a dazuzzukan da ke sassan Najeriya dabam-dabamHoto: AFP/Luis Tato

Kama daga sashen arewacin kasar zuwa na Kudu dai, batu na satar al'umma da karbe kudin fansa na zaman kan gaba cikin jerin rashin tsaron da ke tashi da lafawa. To sai dai kuma wata sanarwar mahukuntan jihar Ondo da ke yankin Kudu maso Yammacin kasar a kan Fulani makiyaya, na shirin bude sabon babi a cikin rikicin noma da kiwon da ke shirin rikidewa ya zuwa na siyasa. Wannan ne dai karo na farko da wata jiha cikin Tarayyar Najeriyar ke fitowa karara, tare da umartar Fulanin da ke sana'ar kiwo a dazukan jihar su tattara su bar cikinta cikin wa'adin mako daya tilo.

Karin Bayani:Najeriya: Kokarin shawo kan rikicin filin noma

To sai dai kuma tuni umarnin ya tayar da hankali cikin Najeriyar, inda gwamnatin kasar ke fadin ba a isa ba. Abujar dai ta ce jihar ta  Ondo koma duk wani sashe na kasar, ba shi da ikon korar duk wani dan kasar da ke bukatar ya zauna cikin wani sashe, a fadar Malam Garba Shehu da ke zaman kakakin fadar gwamnatin Najeriyar. Koma ya zuwa ina idon na gwamnatin ke shirin ya kai da nufin bayar da kariya ga dubbai na Fulani makiyayan da ke fuskantar barazana mai girma dai, matakin jihar ta Ondo na dada nuna alamun rikidewar rashin tsaron kasar ya zuwa na siyasa mai muni.
Jihar ta Ondo dai ta nemi Fulanin da su yi rijistar kansu da nufin tantance aya da tsakuwa a cikin rikicin da sannu a hankali ke sauya sana'ar kiwon zuwa sana'ar satar al'umma. Kuma a fadar Bello Abdullahi Badejo da ke shugabantar kungiyar Miyyetti Allah Kautal Hore a Najeriyar,  Fulanin ba su da niyyar mika kansu a sare walau a jihar Ondo ko kuma a ko'ina da sunan rikici. Rataye kare bisa laifin kura ko kuma kokari na kai karshen annobar sace mutane, sannu a hankali dai ana yi wa Fulani Makiyaya na dazukan kallon barazana mai girma.

'Yan bindiga na satar mutane tare da kai su cikin dazuzzuka domin neman kudin fansaHoto: DW/Katrin Gänsler

Karin Bayani:Gwamnatin Najeriya ta ce babu tilas a shirin Ruga

Tun dai kafin Ondo dai jihar Benue ta nemi haramta harkar kiwon a cikin sunan rashin tsaron da ke ta kara karuwa cikin jihar. Barrister Buhari Yusuf wani lauya ne mai zaman kansa a Abuja fadar gwamnatin Najeriyar, kuma a cewarsa matakin na Ondo ya sabawa sassa dabam-dabam na kundin tsarin mulkin kasar. Akwai dai tsoron rikidewar rikicin rashin tsaron zuwa baka ta siyasa a cikin Najeriyar da ke kara kusantar zabe a cikin ta'azzarar kiyyaya a tsakanin kabilu da masu mabanbamta addinai a kasar.