1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabon

Gabon: Sabon sharadin takarar shugaban kasa

September 25, 2024

Wakilan majalisar rikon kwarya na mulkin soja a kasar Gabon, sun kammala tantance daftarin sabon kundin tsarin mulki da ya bar baya da kura. Tsauraran sharuddan tsayawa takarar shugabancin kasa da suka yi.

Gabun | Janar Brice Oligui Nguema | Zabe
Shugaban gwamnatin mulkin soja ta Gabon Janar Brice Oligui NguemaHoto: AFP/Getty Images

A wani yunkuri na tsara sabon kundin tsarin mulkin kasar Gabon, wakilan al'umma sun bullo da wasu tsauraran sharudda ga 'yan takarar shugaban kasa. Daga yanzu dole ne dan kasa ba wai ya kasance an haife shi a kasar Gabon ne kadai ba, tilas ya tabbatar da cewa iyayensa da kakanninsa duk 'yan asalin kasar ne kafin ya yi zawarcin kujerar mulki. Kazalika, dole ne miji ko matar dan takarar ya cika ko ta cika wadannan tanade-tanade kafin ya ko ta samu damar tsaya wa takara. Sai dai wadannan sababbin tanade-tanade sun haifar da zazzafar muhawara a tsakanin al'ummar Gabon, saboda suna da hatsarin raba kan al'umma tare da mayar da wasu saniyar ware. Ko da  dan jarida kuma mai lura da harkokin siyasa Roy Atiret Biye sai da ya nuna rashin jin dadinsa game da wannan mataki, wanda ya ce yana shirin tsunduma kasar cikin sabon mulkin kama-karya.

Jagoran adawa kana tsohon firaministan kasar Gabon, Alain Claude Bilie By NzéHoto: STEEVE JORDAN/AFP

Shi ma masanin zamantakewa Cyr Pavlov Moussavou na da irin wannan ra'ayi, inda ya ce daftarin sabon kundin tsarin mulkin kasar Gabon na neman mayar da wasu 'yan kasa saniyar ware. Wasu masharhanta na ganin cewa, shakku da ake da shi kan tushen hambararren shugaban kasar Gabon Ali Bongo Ondimba ne ya sa gwamnatin mulkin soja ke neman tsaurara matakan tsaya wa takara a mukami mafi girma a kasar. Amma wani dan kasar Gabon Serge Essone, mai shekaru 32 a duniya, ya yi imanin cewa wannan garambawul kan sharuddan takara zai karfafa kishin kasa. Akasarin shugabannin siyasar Gabon ba su ce uffan ba kan wannan batu mai muhimmanci na takarar shugabancin kasa in ban da dan hamayya kuma tsohon firaminista Alain Claude Bilie By Nzé da ke nuna fargabar cewa wannan sabon matakin zai raba kan 'yan kasar ta Gabon. Amma dole ne majalisar ministoci ta amince da daftarin sake fasalin kundin tsarin mulkin na Gabon, kafin a mika shi domin gudanar da kuri'ar raba gardama a karshen shekara.