1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon shugaban aikin sa ido a Siriya ya isa birnin Damaskus

April 30, 2012

Bayan isarsa birnin Damascus na kasar Siriya Gen. Robert Mood ya yi kira ga bangaroin da ba su ga maciji da juna da su kawo karshen tashin hankali

Major-General Robert Mood, of Norway,is photographed prior to a meeting at the European headquarters of the United Nations in Geneva, Switzerland, Wednesday, April 4, 2012. Major-General Mood will head the planning team that is expected to arrive in Damascus very soon, to discuss the modalities of the eventual deployment of a U.N. supervision and monitoring mission. (Foto:Keystone/Martial Trezzini/AP/dapd).
Robert MoodHoto: AP

Sabon shugaban tawwagar 'yan sa ido ta Majalisar Dinkin Duniya a Siriya, General Robert Mood na kasar Norway ya kama aikinsa yana mai karfafa imanin samun nasara. Bayan isarsa a birnin Damaskus ya ce akwai bukatar kawo karshen tashin hankalin da ake fuskantar a kasar ta Siriya muddin ana bukatar samun nasarar shirin zaman lafiya da kofi Annan, manzon Majalisar Dinkin Duniya na musamman ya gabatar. Mood ya ce jami'an sa ido na majalisar guda 30 ke aiki a Siriya i zuwa yanzu. To amma ya ce za a kara yawansu zuwa sama da 300 nan da wata guda. Ga baki daya jami'an Majalisar Dinkin Duniya guda 300 za a tura zuwa kasar ta Siriya.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Abdullahi Tanko Bala