Sabon shugaban Hezbollah ya ce zai ci gaba da yakar Isra'ila
October 30, 2024Sabon shugaban kungiyar Hezbollah Na'im Qassem ya yi alkwarin ci gaba da yakar Isra’ila, yayin da a daya hannun kuma ya ce a shirye yake ya tsagaita bude wuta bisa wani sharadi. A jawabinsa na farko tun bayan nadin shi, Qassem ya nunar cewar Hezbollah ta fara farfadowa makonni kalilan bayan da Isra'ila ta kashe jagoranta Hassan Nasrallah.
Karin bayani: Hezbollah ta tabbatar da kashe Hassan Nasrallah
Wannan barazanar na zuwa ne a daidai lokacin da Isra'ila ta kara kai hare-hare kan tungar Hezbollah a gabashin Lebanon, inda rundunar sojin Isra'ila ta yi shelar kashe mataimakin kwamanda na rundunar al-Radwan, a wani harin da ta kai a kusa da Nabatiyeh da ke kudancin kasar Labanon. Sai dai a nata bangare, Hezbollah ta yi ikirarin harba jirage marasa matuka da rokoki a wasu cibiyoyin uku na soji a arewacin Isra'ila.
Karin bayani: Rikicin Israila da Hezbollah: Mene ne sirrin kamewar Iran
Ministan makamashin Isra'Ila Eli Cohen ya ce suAna ci gaba da tattaunawa a majalisar tsaron Isra'ila kan sharudan tsagaita wuta a Lebanon, inda Tel Aviv ta bukaci janyewar kungiyar Hezbollah daga kudancin Lebanon, tare da tura sojojin Lebanon kan iyaka da Isra'ila.