An rantsar da sabon shugaban Laberiya
January 22, 2024A wannan Litinin an rantsar da sabon shugaban kasar Laberiya, Joseph Boakai bayan nasarar da ya samu a zaben da aka gudanar inda ya kayar da Shugaba George Weah mai barin gado. Mai shekaru 79 da haihuwa sabon shugaban Boakai da karamar tazara ya lashe zaben na watan Nuwamba inda ya samu wa'adin mulki na shekaru shida.
Shi dai Joseph Boakai ya shafe shekaru 40 a harkokin siyasar kasar ta Laberiya da ke yankin yamamcin Afirka inda ya rike mukaman da suka hada da mataimakin shugaban kasa na tsawon shekaru 12 daga shekara ta 2006 zuwa 2018 karkashin tsohuwar shugabar kasar Ellen Johnson Sirleaf, wadda ta kasance mace ta farko da aka zama kan madafun ikon kasar.
Sabon shugaban kasar ta Laberiya, Joseph Boakai yana da jan aiki kan yaki da talauci gami da cin hanci da rashawa.