1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon shugaban Masar zai fuskanci ƙalubale da dama

June 25, 2012

Ko da shi ke ya yi alƙawarin mayar da Masar tsintsiya maɗaurinki ɗaya, amma kuma batun neman nesanta sojoji daga madafan iko na zama ƙarfen ƙafa ga shugaba Mohammed Mursi.

In this image taken from Egypt State TV, newly-elect President Mohammed Morsi delivers a speech in Cairo, Egypt, Sunday, June 24, 2012. Islamist Mohammed Morsi was declared the winner Sunday in Egypt's first free presidential election in history, closing the tumultuous first phase of a democratic transition and opening a new struggle with the still-dominant military rulers who recently stripped the presidency of most of its powers. (Foto:Egypt State TV/AP/dapd) MANDATORY CREDIT.
Hoto: AP

Wasu daga cikin magoya bayan ƙungiyar 'yan uwa musulmi na ci gaba da bushe bushe. Wasunsu kuwa kaɗa tutar ƙasar Masar suke yi a dandalin Tahrir domin bayyana farin cikinsu game da nasarar da Mohammed Mursi ya yi a zaɓen shugaban ƙasa. Shi dai Mohammed Mursi ya zama shugaban farko da aka zaɓa ƙarƙashin tafarkin demokarɗiyya bayan kifar da gwamnatin kama karya ta Hosni Mubarak. Daɗin daɗawa ma dai, ya tsare wa abokin hamayyarsa Ahmed Shafik, wanda ake dangantawa da ɗan takarar majalisar mulkin soja da ƙuri'u kusan miliyan ɗaya. Kana ya kasance mutumin da shugabannin da suka jagoranci juyin juya hali ciki har da Gaber Rana suka mara wa baya.

"Ina matikar jin dadin kayar da Shafik da aka yi. Abin da ke kara faranta min rai ma, shi ne nasarar Mursi. Wannan ya na nufin cewa juyin juya hali zai ci gaba."

Babban ƙalubalen da ke gaban Mohammed Mursi dai na fitowa ne daga majalisar mulkin sojan Masar, wacce ke da niyar ci gaba da taka rawa a harkokin mulkin ƙasar. Tun a makwannin da suka gabata ne, ta mayar da muƙamin shugaban ƙasa kusan na jeka na yi ka, inda ta sanya sojoji a matsayin waɗanda za su ƙayyade kasafin tsaron ƙasa, tare da kawo gyara ga kundin tsarin mulkin Masar idan zarafi ya kama. Sai dai magoya bayan ƙungiyar 'yan uwa musulmi sun lashi takobin ci gaba da zaman dirshan a dandalin neman 'yanci na Tahrir, har sai sun ga cewar an sakarwa halartaccen shugaba wato Mohammad Mursi wuƙa da naman tafiyar da harkokin mulkin ƙasar Masar. Hamada Abdelaziz da ya shafe kusan mako guda ya na kwana a dandalin Tahrir, ya ce ta hanyar zanga-zangar lumana ne za su ceto juyin juya halin Masar.

Ana ci gaba da zaman dirshan a Tahrir domin neman 'yanciHoto: Reuters

"Zan ci gaba da kwana a dandalin Tahrir matikar ba a biya mana buƙatunmu ba: Ma'ana majalisar mulkin soja ta lashe amanta ta hanyar soke doka da ta fitar. Ta haka ne kawai zan ji ni cikin kwanciyar hankali a Masar."

Ko da shi ke dai Mohammed Mursi mai shekaru 63 da haihuwa bai fito fili ya bayyana hanyoyin da zai bi wajen ƙwaco ikonsa daga hannun sojojin ba, amma dai ana danganta shi da tsohon jemage a fiskar gwagwamar tabbatar da demokraɗiyya a Masar. Shekaru 30 cur zababben shugaban na Masar ya shafe ya na kare manufofin 'yan uwa musulmi. Hasali ma dai wannan kungiya da ya ce zai wanke hannyensa daga cikinta ce ta fi yawan 'yan majalisa a Masar a halin yanzu. Sai dai rinjayen na ƙungiyar da ta tsayar da Mursi ke da shi, ya sa wasu 'yan Masar kallo shugaban tamkar wani mai manufar kafa shari'ar musulunci a ƙasar. Saboda haka ne ma wasu mutane kamar su Amira Salem ke ganin cewa Masar za ta iya faɗawa cikin rigingimu ƙarƙashin shugabancin Mursi.

Minista Westerwelle na Jamus ya kai wa Tantawi na Masar ziyaraHoto: picture alliance/dpa

"Ina da fargaba game da ƙungiyar 'yan uwa musulmi. Mursi zai iya shafe shekaru da dama akan karagar mulki. Saboda haka Masar za ta iya faɗawa cikin matsalolin da ake fiskanta a Iran ko kuma Afghanistan."

Sai dai kuma sabanin wannan hasashe, Mohammed Mursi ya yi alƙawarin naɗa mace ko kuma wani mabiyin darikar Koptik a matsayin firaministansa. Kana ya yi alƙawarin mayar da mayar da Masar tsintsinya maɗaurinki ɗaya.

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Abdullahi Tanko Bala