Sabon shugaban Saliyo ya yi alkawarin hadin kan kasa
April 5, 2018Babban alkalin kasar Saliyo Abdulai Charm shi ne ya rantsar da sabon shugaban Julius Maada Bio a wani Otal da ke Freetown babban birnin kasar.
A jawabinsa bayan rantsar da shi shugaban yace 'wannan ita ce mafarin tafiya. Al'aummar Saliyo sun yin zaben da zai sauya lamura, mun yi farin ciki kuma mun daura niyyar yin aiki a sabuwar gwamnatin Saliyo.'
Dokokin hukumar zaben kasar Saliyo dai sun bada damar kalubalantar zaben cikin kwanaki bakwai bayan sanar da sakamakon zabe a hukumance. Tuni ma dai dan takarar jam'iyyar APC mai mulki Samura Kamara ya baiyana cewa zai kalubalanci sakamakon zaben a kotu.
'Yan uwana 'yan Saliyo, a madadin jam'iyar APC ina mika godiya a gareku na goyon bayan da kuka bamu a wannana tafiya. Kamar yadda kuka sani hukmar zabe ta sanar da sakamako, amma muna sanar da ku cewa ba mu amince da sakamakon ba, bisa dalilan magudi, da aringizon kuri'u da rashin bin tsari wanda mun ja hankalin hukumar zaben tun farko, a don haka a matsin jam'iyya wajibi mu bi ka'idojin da suka wajaba na ganin an yi adalci.'
Sabon shugaban kasar dai, ya karbi ragamar shugabanci ne a dai dai loakcin da kasar ke fama da bakar talauci sakamakon rashin ayyuki da rarrabuwar kan 'yan kasa da kuma kokarin yin katanga da cutar Ebola wadda ta haddasa hasarar rayukan 'yan kasar da dama.
Nasarar Julius Maada Bio, ta zo ne bayan da dukkannin 'yan takarar suka gaza cimma kashi 55 na kuri'u a zagayen farko na zaben da ya gudana a ranar 7 ga watan Maris. Sai dai ga alama tsugune ba ta kare ba, ganin yadda abokin takararsa Samura Kamara ya nuna ja a kan sakamakon da hukumar zaben ta sanar.