1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Abuja: Ziyarar sabon shugaban Senegal

May 16, 2024

A wani abun da ke iya kai wa ga hasashe na makomar yankin yammacin Afirka, sabon shugaban kasar Senegal Bassirou Diomaye Faye ya gana da shugaban Tarayyar Najeriya Bola Ahmed Tinubu a Abuja.

Najeriya | Bola Ahmed Tinubu | Senegal | Bassirou Diomaye Faye | Dangantaka
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da na Senegal Bassirou Diomaye FayeHoto: Jerome Favre/EPA

Duk da cewar dai ya kwashe tsawon kasa da sa'o'i biyu a fadar gwamnatin Tarayyar Najeriya da ke a Abuja, tuni dai ziyarar shugaban kasar ta Senegal Bassirou Diomaye Faye ke dauka tara hankali ciki dama wajen yankin na yammacin Afirka. Duk da cewar dai an kare ganawar a cikin kuryar daki, kimanin ministocin Najeriyar hudu da suka hadar da ministan ciniki da na harkar noma ko bayan ministan harkokin waje da ma kakakin gwamnatin kasar ne suka taka rawa a yayin ganawar. A wani abun da ake yi wa kallon, kokarin ingantar ciniki da kila ma batun harkar noman a tsakanin kasashen biyu.

Karin Bayani: Senegal: Mata basu sami yawan mukamai ba

To sai dai kuma na kan gaba cikin ganawar a fadar Mohammed Idris da ke zaman ministan labarai kuma kakakin gwamnatin Najeriyar, na zaman zawarcin kasashen yankin uku da ke wani bore sakamakon mulkin soja. Ko ya zuwa ina Abujar ke shirin zuwa cikin zawarcin kasashen da ke kawancen Sahel dai, ziyarar da ke zaman irinta ta farkon fari ga shugaban Senegal din da ya hau mulki cikin watan jiya na kuma samun fassara dabam-dabam a tunanin kwarrarun da ke cikin yankin yanzu. Shugaba Faye dai ya hau mulki a kan alkawarin karin 'yancin Senegal dag hannun kasar Faransa da ke zaman uwargijiyar kasashe da yawa a yankin na yammacin Afirka, amma kuma ke fuskantar turjiyar da ke da girman gaske cikin kasashen yankin.

Kasashen Burkina Faso da Mali da Jamhuriyar Nijar na kawancen AES SahelHoto: Fanny Noaro-Kabré/AFP/Getty Images

A yayin kuma da ake kallon wani danyen ganye a tsakanin gwamnatin da ke kan karagar mulki a cikin Najeriya da kasar ta Faransa, a wani abun da ke zaman ba sabun ba. Faruk BB Faruk dai na sharhi cikin batun siyasar yankin, kuma ya ce da kamar wuya Senegal din ta dauki kokarin yin sulhun cikin fadan na Faransa. Duk da cewar dai ana zaman jiran sanarwar fadar gwamnatin kasar da ke a Abuja kan tasirin ziyarar a tsakani na manyan kasashen yankin guda biyu dai, tun da farkon fari shugaba Tinubu bai boye aniyarsa ta dorawa a cikin zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu ba.

Karin Bayani: Zaman tattauna hanyar maslaha a rikicin Mali

Kuma ko bayan sakon taya murna Tinubun ya kasance a Dakar cikin watan jiya, inda ya taka rawa a bikin rantsuwar Shugaba Faye din. Kuma a fadar Ambasada Baka Mohammed da ke zaman tsohon jakadan Najeriyar, sabuwar ziyarar na zaman danbar wani yunkuri na tattaunawa a cikin neman mafitar rigingimun tsaro da ma na siyasar da ke a yankin yanzu. Rawar kasashen biyu dai na iya kai wa ya zuwa sauya makomar ECOWAS ko CEDEAO din da ke cikin rudani, sakamakon tawayen kawayen Sahel da rikicin tsaro da atttalin arzikin da ke dada kamari a tsakanin al'ummar kasashen sama da miliyan sama 400.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani