Sabon tashin hankali a ƙasar Mali
September 30, 2013A ƙasar Mali bayan zaman lafiya da aka samu 'yan watannin da suka gabata, wani sabon tashin hankali ya ɓarke a arewacin ƙasar. Rohotonni suka ce dakarun gwamnati da 'yan tawayen Abzinawa sun gobza faɗa a garin Kidal. Dama dai a 'yan kwanakinnan, an samu faɗace-faɗace nan da can, amma gobzawar ta jiya ita ce ta gaba da gaba mafi ƙarfi da aka samu tun watanni. Tun dai a ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne, Abzinawa ƙarƙashin ƙungiyar MNLA, suka ce sun jingine jarjejeniyar da suka cimma da gwamnati, wanda aka yi tun a watan Juni. 'Yan tawayen sun zargi gwamnati Boubakar Keita da rashin cika ƙa'idar yarjejeniyar da suka cimma a baya. Tun bayan juyin mulki ne dai, 'yan tawayen Abzinawa da mayaƙan Islama suka ƙwace iko da arewacin Mali, kafin ƙasar Faransa ta kai farmakin ƙwato yankin.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammed Nasiru Awal