Soke tsarin sakandare a Najeriya
February 7, 2025Maimakon shekaru guda shida a matakan firamare da wasu guda uku a karama da kuma babbar sakandare dai, Najeriya na shiri na karkata zuwa wasu shekaru har 12 ba hutu.
Kafin kuma su kama hanyar kai wa ga jami'a cikin tsarin 12-4 da gwamnatin kasar ta kai ga sanarwa.
Tsarin kuma da Abujar ke da babban fata zai rage yawan yaran da ba su da damar ilimi cikin kasar. Ya zuwa karshen shekarar da ta shude dai Najeriyar ce take sahun gaba cikin batu na yawan yaran da ba sa cikin aji a duniya baki daya.
To sai dai kuma tun ba'a kai ga ko'ina ba dai sabon tsarin ke fuskantar turjiya ta kwarrarun da ke masa kallon da biyu. A shekara ta 1976 ne dai tarayyar najeriyar ta fara aikida tsarin da Abujar ke neman sauyawa yanzu.
To sai dai kuma shekaru 50 bayan nan yara kusan miliyan 18 ne ke gararramba a gari sakamakon gaza samun damar ilimin a cikin tarayyar Najeriyar, a fadar hukumar yara ta Majalisar Dinke Duniya UNICEF.
Soke tsarin yanzun dai na nufin kai karshen kanana da ma manyan makarantun sakandare a kasar, abun kuma da ke iya hargitsa tsarin ilimin da kila ma shafar makomar dubbai na malaman da ke sana'ar koyarwa a kasar.