Kasashen EU na neman mafita kan batun 'yan gudun hijira
June 22, 2016Talla
Sabon shirin wanda zai dora a kan shirin tsaron gabar tekun kan iyakokin kasashen na Frontex, zai fara aiki ne daga lokacin bazara na wannan shekara, da nufin kare kan iyakokin kasashen na EU. A karkashin shirin dai za a dauki ma'aikata kimanin 1000 da kuma masu tsaron kan iyakokin kasashen 1 500. Wannan sabuwar yarjejeniya dai za a fara aiki da ita da zarar majalisar ministocin Tarayyar Turan ta amince da shi.