1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Nijar: Kaddamar da yaki da Maleriya

Mahaman Kanta LMJ
October 18, 2018

A Jamhuriyar Nijar an kaddamar da sabon tsarin yaki da cutar zazzabin cizon sauro wato Maleriya, wanda shugabannin kasashen Afrika suka bullo da shi.

Mücke Malaria
Hoto: picture-alliance/dpa/P. Pleul

Kungiyar Tarayyar Afirka AU ce dai ta bullo da tsarin tare da bukatar daukacin kasashen nahiyar su rungume shi. Kafin nan da shekara ta 2030 za a yi wa yara jarirai daga haihuwarsu rigakafin kamuwa da cutar zazzabin cizon sauron. A yanzu dai zazzabin na cizon sauro na zaman guda daga cikin cututtuka biyar da suka fi hallaka yara kanana 'yan kasa da shekaru biyar da ma janyo mutuwar mata masu juna biyu kafin da kuma yayin haihuwa. Baya ga wannan ma, kiyasi ya nunar da cewa cutar zazzabin cizon sauron wato maleriya na zaman cuta ta kan gaba da ke haddasa mutuwa fiye da kima a Afirkan.

Cibiyar yaki da cutar zazzabin cizon sauro ta Jamhuriyar ta Nijar da ke karkashin ofishin ministan kiwon lafiya ce dai ta shirya wannan taro. Wakilai da dama daga kasashen Afirka da ma wakili daga kungiyar Tarayyar Afirkan suka halarci taron kaddamar da sabon tsarin yaki da cutar ta zazzabin cizon sauro wato maleriya, inda daga bisanin dukkanin kasashen nahiyar Afirkan za su fara gudanar da tsarin a kasashensu.

 

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani