Sabon yanayin siyasa a Isra'ila.
December 21, 2005A lokacin da likitoci suka sallame shi daga asibiti, Firamiyan Isra’ila Ariel Sharon, ya fito ne yana murmushi ga maneman labaran da suka taru suna daukar hotonsa, suna kuma neman su yi masa tambayoyi. Bisa dukkan alamu dai, zaban Benjamin Netanyahu, tamkar sabon shugaban jam’iyyar Likud da aka yi na daya daga cikin abin da ke faranta wa Sharon rai. Saboda fatarsa ce, ya yi gwagwarmaya da Netayanhun a fagen yakin neman zabe, wanda za a gudanar a cikin watan Maris na shekarar badi.
Masu lura da al’amuran da ke kai suna kawowa a Isra’ilan sun ce kasancewar Netayanhu, a shugabancin jam’iyyar Likud, kuma dan takaranta a zaben, zai bai wa Sharon damar gabatar wa masu ka da kuri’u, sabuwar jam’iyyar „Kadima“ da ya kafa, tamkar wani zabi gare su, wadda ta bambanta da jam’iyyar masu bin ra’ayin rikau ta Likud. A halin yanzu dai, jama’a da dama na kasar Isra’ilan na ganin jam’iyyar Likud din ne tamkar `yan mazan jiya, wadanda har ila yau ba su fahimci cewa, wanzuwar Isra’ila tamkar kasar Yahudawa da kuma kasa mai bin tafarkin dimukradiyya ta dogara ne kacokan, kan yadda za ta yi zaman makwabtaka na cude ni in cude ka da al’umman Falasdinu.
Babu dai sauran wata wata kuma. Taswirar sauyi, ta yanayin siyasar Isra’ila, ta zayyanu sosai, kuma kome na shimfide dalla-dalla. Masu zabe za su iya sanin irin manufar da ko wace jam’iyya ke bi da kuma inda suka mai da alkiblarsu. Da can dai, ba haka yanayin yake ba.
A lal misali, da can jam’iyyar Likud ce jam’iyyar `yan tsageru masu kishin kasa, wadanda ke da burin maido da duk harabar Falasdinu karkashin ikonsu. Sabili da haka ne ma jam’iyyar ta fi goyon bayan shirin gina matsugunan Yahudawa a yankunan Falasdinawan da Isra’ilan ta mamaye. Amma sai aka wayi gari, daya daga cikin kusoshinta, kuma rikakken dan mazan jiya, wato Ariel Sharon, ya canza sheka, ya aiwatad da shirin janye dakarun kasar bani Yahudun da kuma ta da matsugunan Yahudawa gaba daya daga zirin Gaza.
A daya bangaren kuma, da can jam’iyyar Labour ce ake kwatanta ta da nuna sassaucin ra’ayi da kuma neman zaman lafiya. Amma, sai kwatsam shugabanta Shimon Perez, ya shiga gwamnatin Ariel Shharon, inda wato yake dauke da allhakin wasu munanan hare-haren da dakarun Isra’ilan suka kai kan Falasdinawa. Wadannan misalan biyu dai sun janyo rudami a bainar jama’ar kasar Yahudun. Duk kuma ba a san irin kamun ludayin da jam’iyyun ke yi ba.
To yanzu kuwa al’amura sun canza. Shi Shimon Pererz ya fice daga jam’iyyar Labourn, ya hada gwiwa da Sharon a sabuwar jam’iyyar „Kadima“ da ya kafa. Shi ko Sharon, bayan ficewarsa daga jam’iyyar Likud din da kafa wata sabuwar jam’iyya, burinsa ne ya ci gaba da manufofinsa na janyewa daga wasu yankunan Falasdinawan, da kuma mai da wasu, kamar a Gabar Yamma tamkar harabar Isra’ila don karre maslaharta.
Nazarin taswirar yanayin siyasar Isra’ilan, kamar yadda take a halin yanzu na nuna cewa, akwai jam’iyyu guda 3 ko wacce, mai manufofinta, wadanda suka bambanta dalla-dalla da na sauran. Da farko dai, jam’iyyar Kadima ta Sharon, wato ta dukufa ne wajen zayyana wa Isra’ila iyakarta a Gabas, ba tare da tuntubar Falasdinawa ba. Ita ko jam’iyyar Labour, karkashin jagorancin sabon shugabanta Amir Peretz, manufarta ce sulhunta duk rikice-rikicn yankin ta hanyar tuntubar juna da shawarwari da Falasdinawa. Jam’iyyar Likud kuwa, karkashin jagorancin Benjamin Netanyahu, har ila yau tana matukar adawa ne da duk wani yunkuri na janyewa daga yankunan Falasdinawan da ta mamaye.
To yanzu dai za a iya cewa, an share fagen gudanad da sabon zabe a Isra’ila, kuma masu ka da kuri’un na da cikakkiyar masaniya game da inda ko wace jam’iyya ta mai da alkiblarta. Ta hakan ne kuma za su iya yanke wa kansu shawara kan jam’iyyar da za su ka da wa kuri’unsu.