Sabon zargi akan shirin nukiliyar Iran
June 6, 2012Shugaban Mahmoud Ahmadinejad na ƙasar Iran ya zargi manyan ƙasashen yammacin duniya da nemo hanyoyin da za su kawo cikas da kuma ɓata lokaci game da batun shirin nukiliyarta da ake taƙaddama akansa. Shugaban na Iran Mahmoud Ahmadinejad, wanda ke magana a birnin Beijing fadar gwamnatin ƙasar China, ya ce a shirye Iran take ta shiga cikin tattaunawa a birnin Moscow na ƙasar Rasha ko kuma ma a birnin Beijing na ƙasar China, kuma tuni ta gabatar da kyakkyawan tayi game da hakan.
Shugaban na Iran yana tsokaci ne game da tattaunawar da manyan ƙasashe biyar dake da kujerar din-din-din a kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya da kuma Jamus za su yi tare da ita a birnin Moscow nan gaba kaɗan cikin watan Yunin nan da muke ciki. Ƙasashen yammacin duniya na zargin Iran da ƙoƙarin ƙera makaman ƙare dangi a yayin da ita kuwa take nanata cewar domin samar da makamashi ga al'umma ne.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman