1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabuwar barazanar harin ta'addanci a Turai

Gazali Abdou TasawaApril 19, 2016

Hukumar kula da auna girman barazanar yiwuwar kai wa kasar Beljiyam harin ta'addanci ta ce yanzu haka akwai tarin mayakan sa kai 'yan asalin kasashen ketare a Siriya da ke neman shigowa kasashen Turai dan kai hari

Italien Rom Sicherheitskräfte vor Kolloseum
Hoto: Getty Images/AFP/A. Pizzoli

Hukumar kula da auna girman barazanar yiwuwar kai wa kasar Beljiyam harin ta'addanci ta Ocam ta ce yanzu haka akwai tarin mayakan sa kai 'yan asalin kasashen ketare a Siriya da ke neman shigowa kasashen Turai musamman a kasar Belgiyam domin kaddamar da hare-haren ta'addanci.

Daraktan wannan hukuma wato Paul Van Tigchlt ne ya sanar da hakan a wannan Talata a lokacin wani taron manema labarai. Wannan sabuwar barazana na zuwa ne makonni hudu bayan harin ta'addancin da mayakan kungiyoyin da ke kiran kansu 'yan jihadi suka kai a birnin Brussels inda suka hallaka mutane 32 da kuma jikkata wasu 340.

Hukumar ta Ocam ta ce lalle an dauki karin matakai na tsaro da bincike tun daga wancan lokaci, amma duk da haka akwai barazanar yiwuwar sake fuskantar irin wadannan hare-hare na ta'addanci a kasashen na Turai, musamman a guraren da suka hada da filayen jiragen sama da tashoshin jiragen kasa da na sauran motocin safa da kuma tashoshin nukliya da kuma manyan shaguna da kasuwanni ko kuma sauran guraren taruwar jama'a kamar gidajen sinema da filayen wasanni.